Adadin mutanen da suka mutu a yakin da Isra'ila ke yi a Gaza ya kai 45,805, yayin da aka kashe karin mutane 88 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, in ji ma'aikatar lafiya ta Falasɗinu a yankin.
Haka kuma mutum 208 suka jikkata a hare-haren da sojojin Isra'ila suka kai a sassa daban-daban na Gaza, in ji ma'aikatar.
Sanarwar ta kuma ce, adadin wadanda suka jikkata daga mamayar Isra'ila ya karu zuwa 109,064.
Ma'aikatar ta kuma sake nanata cewa har yanzu akwai gawawwaki da suke maƙale a karkashin baraguzan ginin da kuma gefen titina.
2108 GMT — Isra'ila ta kashe 'yan jarida 10 a watan Disamba a Falasɗinu
Adadin mutanen da suka mutu a yakin da Isra'ila ke yi a Gaza ya kai 45,805, yayin da aka kashe karin mutane 88 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, in ji ma'aikatar lafiya ta Falasɗinu a yankin.
Haka kuma mutum 208 suka jikkata a hare-haren da sojojin Isra'ila suka kai a sassa daban-daban na Gaza, in ji ma'aikatar.
Sanarwar ta kuma ce, adadin wadanda suka jikkata daga mamayar Isra'ila ya karu zuwa 109,064. Ma'aikatar ta kuma sake nanata cewa har yanzu akwai gawawwaki da suke maƙale a karkashin baraguzan ginin da kuma gefen titina.
2108 GMT — Kungiyar 'yan jarida ta Falasɗinu ta ce Isra'ila ta kashe 'yan jarida akalla 10 a cikin watan Disamba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na WAFA ya ruwaito.
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta bayyana cewa sojojin Isra'ila sun aikata laifuka 84 a kan 'yan jaridar Falasdinu a cikin watan da ya gabata.
Hukumar ta ce biyar daga cikin wadanda aka kashe, an kashe su ne a wani mummunan harin da aka kai a cikin motar tafi-da-gidanka wadda ke watsa shirye-shiryen talabijin kai-tsaye.
2312 GMT — Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kakkaɓo wani makami mai linzami da aka harbo daga Yemen.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kakkaɓo wani makami mai linzami da aka harba daga kasar Yeman, jim kaɗan bayan jiniya ta fara kaɗawa.
A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ta kafar sadarwa ta Telegram ta ce "Bayan sautin jiniya da aka ji ba da jimawa ba a Talmei Elazar, an kakkaɓo wani makami mai linzami da aka harba daga kasar Yemen kafin ya tsallaka zuwa cikin kasar Isra'ila."
2029 GMT — Isra’ila ta kashe mutum 30 a Gaza a daidai lokacin da aka ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar tsagaita wuta
Isra'ila ta tabbatar da cewa ta ci gaba da tattaunawa a Qatar kan yarjejeniyar tsagaita wuta da Gaza da kuma sakin waɗanda aka yin yi garkuwa da su, yayin da masu aikin ceto suka ce fiye da mutane 30 ne suka mutu a wani sabon harin bam da Isra’ilar ta kai a Gaza da ta yi wa ƙawanya.
Hukumar tsaron farar hula ta ce wani harin da aka kai ta sama a gidan iyalan al Ghoula da ke birnin Gaza ya kashe mutane 11, bakwai daga cikinsu kananan yara.
Katz ya ce Firaminista Benjamin Netanyahu ya ba da "cikakken umarni don ci gaba da tattaunawar".