Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya gurfana a gaban kotu, bisa zarginsa da laifin karbar kudade ba bisa ka’ida ba daga tsohon shugaban kasar Libya Muammar Gaddafi, saboda nasarar da ya yi ta neman shugabancin kasar a shekara ta 2007.
Sarkozy wanda ya samu tattaunawa da lauyoyi da sauran wadanda ake tuhuma a harabar kotun kafin a fara sauraren karar a ranar Litinin, ya sha musanta zargin.
Tsohon shugaban na fuskantar tuhume-tuhume da suka hada da "boye batun almubazzaranci da dukiyar jama'a, da cin hanci da rashawa, da bayar da kudaden yakin neman zabe ba bisa ka'ida ba, da kuma hada baki wajen aikata laifi," in ji ofishin mai shigar da kara na harkokin kudi.
An fara shari'ar ne da karfe 1230 agogon GMT kuma za a shafe watanni uku ana yi. Shari'ar na iya ƙara dagula ƙwarin gwiwar jama'a a fagen siyasar Faransa.
Masu binciken sun yi zargin cewa ya kulla wata yarjejeniya ta cin hanci da rashawa da gwamnatin Libya.
Wannan batu dai shi ne wani al'amari mai cike da rudani da ake zargin ya hada da 'yan leken asirin Libya, da dillalan makamai da kuma zargin Gaddafi ya bai wa shirin yakin neman zaben Sarkozy da miliyoyin Yuro da aka tura zuwa birnin Paris a cikin akwatuna.
Lauyan Sarkozy ya ce shari'ar da ake yi wa tsohon shugaban ƙage ce kawai, kuma babu wani tallafin da Libya ta bayar a yakin neman zabe.
"Bayan shekaru 10 ana bincike, tare da tura kayan aiki da ba a taɓa ganin irinsu ba, da na'urar sauraron waya da ɗaukar nauyin tafiye-tafiyen alkalai zuwa ƙasashen duniya, ba a samu wata alamar kashe kuɗaɗe ba, ko biyan kuɗi kai ko da 'yar ƙaramar hujja ta ɗaukar nauyin kamfe ɗin," in ji lauyansa Christophe Ingrain.
Jerin shari'o'i
Idan aka sami Sarkozy da laifin, zai iya fuskantar daurin shekaru 10 a gidan yari da kuma tarar dala 386,000.
A 'yan shekarun nan Sarkozy ya fuskanci jerin shari'o'i.
A cikin watan Disamba, Kotun Ƙolin Faransa ta amince da hukuncin da aka yanke masa na cin hanci da rashawa da kuma yin tasiri wajen yin fatauci don samun tagomashi daga alkali.
An umurci Sarkozy ya sanya abin hannu na lantarki na tsawon shekara guda a maimakon zuwa gidan yari, wanda shi ne na farko ga tsohon shugaban kasar Faransa.
Masu shigar da kara na harkokin kudi sun ce a shekara ta 2005, Sarkozy, ministan harkokin cikin gida na Faransa a lokacin, ya kulla yarjejeniya da Gaddafi, domin samun kudaden yakin neman zabe, domin tallafa wa gwamnati a fagen kasa da kasa inda aka ware ta.
An kuma tumɓuke tare da kashe Gaddafi a shekara ta 2011.
Daga cikin mutum 12 da ke fuskantar shari'a a cikin tuhumar akwai tsohon na hannun daman Sarkozy Claude Gueant, da tsohon ministan harkokin cikin gida Brice Hortefeux da kuma shugaban yakin neman zabensa na lokacin Eric Woerth, dukkansu ukun sun hallara a gaban kotun a ranar Litinin.