Jam'iyyar Popular Front ta Ƙwatar 'Yancin Falasdinawa (PFLP) ta kira harin harbe-harben a matsayin "saƙo mai ƙarfi" ga mamayar Isra'ila. / Hoto: AFP

Litinin, 6 ga watan Janairu, 2025

1325 GMT — Bangarorin Falasdinawa sun yi kira da a ƙkara ƙaimi wajen yin tirjiya a yankin Yammacin Kogin Jordan da Yahudawa suka mamaye a matsayin ramuwar gayya ga yakin kisan kare dangi da Isra’ila ta yi a Gaza.

Wasu Yahudawa 'yan-kama-wuri-zauna uku aka kashe tare da jikkata wasu 6 a safiyar yau Litinin a wasu harbe-harbe da aka yi a kusa da unguwar Kedumim da ke arewacin Gabar Yammacin Kogin Jordan.

Hamas ta yaba da harin "a matsayin martanin jarumtaka ga ci gaba da laifuka da yakin ƙare dangi da Isra'ila take yi kan al'ummarmu a Gaza, da shirin korar mutane a Yammacin Gabar Kogin Jordan, da kuma hare-haren wuce gona da iri kan Masallacin Ƙudus mai tsarki."

Jam'iyyar Popular Front ta Ƙwatar 'Yancin Falasdinawa (PFLP) ta kira harin harbe-harben a matsayin "saƙo mai ƙarfi" ga mamayar Isra'ila.

Ya yi kira da a bunkasa ayyukan juriya a Yammacin Kogin Jordan "don rikitar da lissafin mamaya da raunana tsarin tsaro."

Fitattun kwamitocin 'yan turjiya sun kira harin "martani ne na dabi'a" ga yakin kisan gillar da Isra'ila ke yi a Gaza da ƙwace yankuna a Yammacin Gabar Kogin Jordan.

11:15 GMT — Isra'ila ta jikkata mutum 40 a harin da ta kai wata makaranta a Gaza

Akalla Falasdinawa 40 ne suka jikkata sakamakon wani harin da jirage marasa matuƙa na Isra'ila suka kai kan wata makaranta da ta kasance mafaka ga fararen hula a yankin zirin Gaza a ranar Litinin, in ji ma'aikatan lafiya.

Shaidu sun ce jiragen yakin Isra'ila sun jefa gurneti kan wata makaranta da ke sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza.

Asibitin Al-Awda ya tabbatar da cewa an kawo mutane 40 bayan harin.

0600 GMT — An koma teburin tattaunawa a Qatar game da tsagaita wuta da sakin mutane da aka yi garkuwa da su a Gaza a yayin da Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta a Gaza.

Masu shiga tsakani na Qatar, Masar da Amurka sun kwashe watanni suna ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin Gaza. Ana yin wannan tattaunawa ce kafin Donald Trump ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Amurka ranar 20 ga watan Janairu.

Ana tattaunawar ce a yayin da Isra'ila ta ci gaba da yin luguden wuta a Gaza ranar Lahadi, inda ta kashe mutane da dama.

2030 GMT — Isra'ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa aƙalla12 tare da jikkata gommai a hare-haren da ta kai a yankuna da dama na Gaza.

An kashe mutum uku ne lokacin da jirgi mara matuƙi ya kai hari a kan babur ɗinsu a arewacin Rafah da ke kudancin Gaza, kamar yadda ma'aikatan kiwon lafiya suka shaida wa Anadolu Agency.

Kazalika wasu majiyoyi sun ce an kashe Falasɗinawa huɗu a harin da Isra'ila ta kai ofishin 'yan sanda na Asdaa da ke Khan Younis.

Bugu da ƙari an kashe Falasɗinawa biyu tare da jikkata wasu da dama a a harin da dakarun Isra'ila suka kai kan wani rukuni na jama'a a yankin Abasan Al-Kabira da ke gabashin Khan Younis.

Wata sanarwa da asibitin Al Awda ya fitar ta ce an kai hari ta sama a gidan iyalan Abu Jarboa da ke sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat inda Isra'ila ta kashe Falasɗinawa biyu.

A Birnin Gaza, Isra'ila ta kashe wani Bafalasɗine, tare da jikkata gommai a wani hari ta sama da ta kai a taron jama'a a unguwar Shujaiyya da ke gabashin birnin.

Wasu mata na alhinin kisan da Isra'ila ta yi wa 'yan'uwansu wadanda aka kai Asibitin Al-Awda. / Hoto: AA

TRT World