Isra'ila na ci gaba da kashe Falasɗinawa a kullum waɗanda akasarinsu yara ne da mata. / Hoto: Reuters

1208 GMT Aƙalla Falasɗinawa 15 Isra’ila ta ƙara kama a wani samame da ta kai a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da ta mamaye, kamar yadda wata ƙungiya da ke kula da fursunoni ta tabbatar a ranar Lahadi.

Sojojin sun kai samamen ne a Hebron da Tubas da Ramallah da Birnin Kudus, kamar yadda hukumar da ke kula da waɗandake tsare da kuma ƙungiyar kula da fursunoni Falasɗinawa suka bayyana a wata sanarwa ta haɗin gwiwa.

“Waɗanda aka kama na fuskantar cin zarafi da duka, da kuma barazana ga iyalansu, baya ga yawaitar ayyukan zagon kasa da lalata gidajen 'yan kasar,” kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.

Kamen na ranar Lahadi ya kawo adadin Falasdinawan da Isra’ila ta kama tun daga 7 ga watan Oktoba a Yammacin Kogin Jordan zuwa 9,550 a cewar alkaluman Falasdinawa.

0602 GMT — Dakarun Isra'ila sun kama Falasɗinawa 16 a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan

Dakarun Isra'ila sun kai samame a garin Silwad da ke arewa maso gabashin birnin Ramallah na Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye sannan suka kama Falasɗinawa 16, a cewar wasu majiyoyi.

Majiyoyin sun ruwaito cewa dakarun Isra'ila sun gudanar da gagarumi samame tare da yin bincike ƙwaƙwaf a cikin gidajen jama'a da dama a garin, inda suka lalata wasu gidajen tare da kayayyakin amfanin jama'a da motoci, sannan suka musgna wa jama'a da yawa.

Daga nan suka kama matasa 16 a garin, suka tafi da su wani wuri da ba a san ko ina ba ne.

2300 GMT — Hamas ta yi tir da hare-haren da Isra'ila take kai wa makarantun Falasɗinawa

Ƙungiyar Hamas mai fafutukar kare hakkin Falasɗinawa ta yi Allah wadai da "sabon laifi" da Isra'ila take aikatawa inda take kai hari a makarantun da ke ƙarƙashin kulawar MDD waɗanda 'yan gudun hijirar da ta kora daga gidajensu suke samun mafaka

“Luguden wutar da sojojin 'yan ta'adda masu mamaya suka yi a makarantar al-Jaouni, wadda ke ƙarƙashin Hukumar Kula da Falasɗinawa 'Yan Gudun Hijira ta MDD mai suna UNRWA inda dubban fararen-hula suke samun mafaka, kisan kiyashi ne kuma wani sabon laifi ne da maƙiya suka aikata, a wani ɓangare na ci gaba da kisan ƙare-dangi kan al'ummar Gaza,” in ji wata sanarwa da ta fitar.

Hamas ta buƙaci ƙasashen duniya da MDD su “ɗauki mataki nan-take domin dakatar da keta hakkokin mutane da kuma aikata laifukan yaƙi, sannan su ɗauki matakai masu ƙwari don hana dakarun masu kaifin kishin kafa ƙasar Isra'ila daga ci gaba da kashe al'ummar Gaza da ba su da madogara.”

Tun da farko Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Gaza ta ce dakarun Isra'ila sun aiwatar da “kisan kiyashi” a makarantar da ke sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat a tsakiyar Gaza, inda suka kashe Falasɗinawa 16 sannan suka jikkata 50.

A gefe guda, ofishin watsa labarai na gwamnatin Gaza ya ce Isra'ila ta kai hari a makarantu 17 da 'yan gudun hijira suke samun mafaka tun daga ranar 7 ga watan Oktoba da ta ƙaddamar da hare-hare a yankin.

Falasɗinawa suna samun mafaka a makarantu saboda Isra'ila tana luguden wuta a gidajensu abin da ya tilasta musu ficewa daga cikinsu. / Hoto: AFP

0010GMT — Hezbollah ta ce ta kai hari a yankin Rasat al-Alam na Isra'ila da ke tsaunukan Lebanon

Hezbollah ta sanar da cewa ta kai hari a wani yankin Lebanon mai tsaunuka da ke Kafr Shuba kuma ta cim ma burinta.

A wani saƙo da ƙungiyar da ke Lebanon ta wallafa a Telegram ta ce ta kai harin rokoki a Rasat al-Alam.

Ta ƙara da cewa ta kai harin ne domin ci gaba da nuna goyon baya ga Falasɗinawan Gaza.

Kawo yanzu rundunar sojin Isra'ila ba ta ce uffan ba game da wannan ikirari na Hezbollah.

Ƙungiyoyin da ke Lebanon da na Falasɗinu, musamman ƙungiyar Hezbollah, sun daɗe suna kai hare-hare kan sojojin Isra'ila a yankin Blue Line tun 8 ga watan Oktoba, inda ɗaruruwan mutane suka mutu sannan wasu suka jikkata, a ɓangaren Lebanon.

TRT Afrika da abokan hulda