Wani hoto da aka ɗauka ta sama ya nuna Aansanin Jiragen Sama na Nevatim bayan harin makamai masu linzami na da Iran ta kai wa Isra'ila. / Hoto: Reuters

Washington DC — Hare-haren makamai masu linzami na baya-bayannan da Iran ta kai wa Isra'ila sun girgiza Gabas ta Tsakiya sun kuma sauya al'amuran tsaron yankin cikin gaggawa.

Yayin da masana ke fashin baƙi kan ƙarfin soji na Iran da kuma yiwuwar sauya dabarunta, ana kuma ƙara tunanin cewa zaɓar wajen da aka kai hare-haren zai taka muhimmiyar rawa wajen tantance sakamakon da duk wani hari na nan gaba zai haifar.

"Akwai ƙarin abubuwa na ƙarfi da Iraniyawa za su iya aiwatarwa wajen yaƙin. Sai dai babban sauyin dabara shi ne idan suka zaɓi wasu wuraren da za su kai hari, su sauya daga kai hare-hare filayen tashin jiragen sama da cibiyoyin tattara bayanan sirri zuwa kai hare-hare cikin birane," kamar yadda Fabian Hinz, wani ƙwararre a Cibiyar Ƙasa da Ƙasa kan Dabaru da Tsare-Tsare ya shaida wa TRT Wolrd.

Ya ce, "Iran ta shafe kusan shekaru 30 tana kashe maƙudan kuɗaɗe wajen bunƙasa manyan makamai masu linzami, don cike giɓin da take da shi na rashin ƙarfin jiragen yaƙi da za su iya tunkarar manyan waɗanda suka yi nisa a fasaha, kamar Amurka da Isra'ila."

Sakamakon hare-haren ranar 1 ga Oktoba, makamai masu linzami na Iran sun samu damar kauce wa tsarin tsaro na Isra'ila.

Hotunan da aka ɗauka ta sama da kamfanin dillacin labarai na Associated Press AP ya wallafa, sun nuna yadda makaman Iran da dama suka sauka a Sansanin Jiragen Yaƙi na Nevatim, wanda ya haɗa da makamai masu linzami fiye da 180.

"Da alama makaman ba su yi wata ɓarna ta a-zo-agani ba, saboda ba lallai makaman sun iya sauka kan ainihin inda aka nufa ba," a cewar Hinz.

Yayin da aka ɗan yi wa Sansanin na Nevatim illa, illar ba za ta shafi irin shirin da Tel Aviv take da shi na yaƙi ba.

Jerin Hare-hare da za a jima ana kaiwa.

Sauyin dabarun kai hare-hare masu linzami na Iran ya sa hankula sun karkata kan ko Isra'ila za ta iya jure — idan yaƙin ya yi tsawo — dogon lokaci ana kai mata jerin hare-hare.

Hinz, wanda kuma ƙwararre ne kan sanin wurare, ya ce "tsarin Tsaron Isra'ila na makamai masu linzami ya ƙunshi matakai daban-daban," da suka haɗa da Iron Dome, da David's Sling, da kuma Arrow 2 da 3 don tare barazanar makamai masu linzami daban-daban.

Sai dai ya yi gargaɗin cewa, "Lokacin da aka kai hari da makamai masu linzami da yawa a lokaci guda, ba lallai ne tsarin na tare makamai mai linzami ya iya fuskantar ƙalubalen ba."

Yayin da Iran ke fatan rikita tsaron Isra'ila ta hanyar amfani da makamai masu linzami da dama da aka inganta su, bazaranar na ƙara yawa. Nan gaba zai iya kasancewa jerin makamai masu linzami ne, sai dai babbar tambayar har yanzu ita ce, shin Isra'ila za ta iya jajircewa?

Harin baya-bayannan na ba-zata ya nuna irin tasiri da karfin makamai masu linzami masu gajeren zango na Iran.

"Makamai masu linzami masu gajeren zango na Iran sun nuna cewa suna sauka daidai inda aka harba su." a cewar Hinz, yana gwada tasirinsa da makaman masu dogon zango.

"Harin da Iran ta kai wa Isra'ila da makami mai dogon zango ya nuna ba su fiya sauka daidai inda aka harba su ba, a cewarsa, yana nuna cewa ko dai saboda matsalar na'ura ta iya sauka daidai inda aka harba idan akwai nisa sosai, ko kuma saboda matakan da Isra'ila take ɗauka na lalata tsarin da ke yi wa makamin mai linzami jagora kan inda zai sauka.

TRT World