Ma'aikatar Harkokin Addini a Gaza ta sanar da cewa Isra'ila ta ruguza kashi 79 cikin 100 na masallatai a Gaza, yayin yaƙin ƙare-dangi da take kan Falasɗinawa.
Sojojin Isra'ila sun yi fata-fata ka masallatai 814 cikin 1,245 da ke Gaza, kuma sun lalata wasu 148 lokacin ruwan bama-baman da ta yi, kamar yadda ma'aikatar ta bayyana ranar Asabar.
Baya ga masallatai, an ruguza coci-coci uku, sannan an lahanta 19 cikin 60 na maƙabartu da gangan, cewar sanarwar.
Ƙiyasin kuɗin da aka yi na asarar na kadarorin ma'aikatar, ya kai dala miliyan $350, in ji su.
Ma'aikatar kuma ta ce sojojin Isra'ila sun wulaƙanta ƙaburbura, sun tono gawarwaki, kuma sun aikata mummunar ta'asa kan waɗanda suka mutu, kamar satar gawarwaki da wulaƙanta jikin matattu.
Baya ga lalata wuraren ibada, ma'aikatar ta ce an rusa gine-gine 11 na ofisoshin gudanarwa na da cibiyoyin ilimi da ke ƙarƙashinta, wanda ke zaman kashi 79 na irin waɗannan gine-gine a Gaza.
'Yaƙin ƙare-dangi'
Ma'aikatar ta ce dakarun Isra'ila sun kashe ma'aikatanta 238 kuma sun kama guda 19 yayin mamaya ta ƙasa a cikin iyakokinta.
Ma'aikatar ta yi tir da hare-hare kan wuraren ibada a Gaza, kuma ta nemi al'ummar duniya, ciki har da gwamnatocin ƙasashe da ƙungiyoyin Musulunci, da su kawo ɗauki nan-take don dakatar da "yaƙin ƙare-dangi da ke gudana."
Isra'ila ta ci gaba da ta'annati a yaƙinta kan Gaza bayan, harin Hamas na 7 ga Oktoba, duk da ƙudurin Kwamitin Tsaro na MDD da ke kiran gaggauta tsagaita wuta.
Sama da mutane 41,820 sun halaka tun lokacin da dakarun Isra'ila suka fara hare-hare, yawancin waɗanda suka mutu mata ne da yara, yayin da wasu 96,800 suka jikkata, cewar hukomomin lafiya na yankin.
Farmakin Isra'ila ya tagayyara kusan duka al'ummar yankin, baya ga hana shiga yankin da ta yi, wanda ya haifar da ƙarancin abinci, tsaftataccen ruwa, da magunguna.
Isra'ila na fuskantar zargin kisan ƙare dangi a Kotun Duniya kan zaluncin da ta yi a Gaza.