Tehran fired around 200 missiles at Israel overnight

0300 GMT — Iran ta sha alwashin kai hare-hare a kan kayayyakin Isra'ila

Shugaban rundunar sojojin Iran ya sha alwashin kai hare-hare a dukkan kayayyakin Isra'ila a fadin ƙasar muddin aka kai musu hari, bayan mahukunta a Tehran sun kai hari da makamai masu linzami kusan 200 a Isra'ila, wacce take kisan ƙara-dangi a yankin Gaza da kai hare-hare a Lebanon.

Za a "kai manyan hare-hare masu ƙarfi kan dukkan kayayyakin Isra'ila," in ji Manjo Janar Mohammad Bagheri a jawabin da ya yi ta gidan talbijin.

Za a "kai manyan hare-hare masu ƙarfi kan dukkan kayayyakin Isra'ila," in ji Manjo Janar Mohammad Bagheri a jawabin da ya yi ta gidan talbijin.

2220 GMT –– Netanyahu ya ce Iran za ta 'ɗanɗana kuɗarta' kan hare-haren makamai masu linzami da ta kai wa Isra'ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce Iran ta yi "babban kuskure" kuma "za ta ɗanɗana kuɗarta kan abin da ta yi".

"Iran ta tafka babban kuskure kuma ɗanɗana kuɗarta," in ji Netanyahu awanni kaɗan bayan Iran ta kai musu hari, sannan ya yi gargaɗi cewa: "Duk wanda ya kai mana hari, za mu rama."

A wata sanarwa ta daban, Ministan Tsaron Isra'ila Yoav Gallant, wanda yake cibiyar bayar da umarnin soji inda yake sanya ido kan kawar da makamai masu linzami da Iran ta harba musu, ya sha alwashin ɗaukar fansa a kanta,

Hakan na zuwa ne bayan mai magana da yawun sojin Isra'ila Daniel Hagari ya sha alwashin "ci gaba da kai hare-hare masu ƙarfi a Gabas ta Tsakiya".

Makamai masu linzami na Iran sun nufi yankunan soji da jami'an tsaro, in ji IRGC. / Hoto: AA

2102 GMT –– Amurka ta yi wa Iran barazana, tana alfaharin cewa ta kare Isra'ila

Mai bai wa Amurka Shawara Kan Harkokin Tsaro Jake Sullivan ya ce harin makamai masu linzami da Iran ta kai kan Isra'ila "da alama bai yi nasara ba kuma bai yi tasiri ba."

Sullivan ya shaida wa manema labarai cewa, Iran ta harba makami mai linzami kusan 200 kan Isra'ila, wadanda Amurka ta yi aiki tare da sojojin Isra'ila wajen katse su, ciki har da yin amfani da jiragen ruwan yaƙi masu lalata abu wajen harba makamai don harbo makamai masu linzami da ke shiga."

"Har yanzu muna aiki tare da IDF da hukumomi a Isra'ila don tantance tasirin harin. Amma a wannan lokacin, kuma ina jaddadawa a wannan lokacin, babu wanda muka san ya mutu a Isra'ila," in ji Sullivan a Fadar White House, inda ya kara da cewa rahotannin farko sun nuna an kashe wani Bafalasdine a Jericho.

"Da farko dai, sakamakon ƙwarewa ta IDF, amma ba shi kadai ba, har da ƙwarewar aikin sojan Amurka da kuma tsayayyen tsare-tsare na haɗin gwiwa na zaton dama za a kai harin," in ji shi.

Ya jaddada cewa gwamnatin Biden ta yi alfahari da kokarin da take yi na kare Isra'ila, yana mai nanata gargadin da wani babban jami'in Fadar White House ya yi cewa Iran za ta fuskanci "mummunan sakamako" kan harin.

"Za mu yi aiki tare da Isra'ila don tabbatar da hakan," in ji shi.

A cikin watan Afrilun wannan shekara bayan wani hari makamancin wannan da Iran ta kai wa Isra’ila, shugaban Amurka Joe Biden ya ƙi goyon bayan wani gagarumin martani da Isra’ila ta mayar kan harin makami mai linzami da Iran ta yi, ya kuma shaida wa Benjamin Netanyahu a lokacin cewa, “Idan ka kai wani babban hari kan Iran, to ka ji da kanka babu ruwanmu.”

Amurka ta yi wa Iran barazana, tana alfaharin cewa ta kare Isra'ila. Hoto: AA / Photo: AFP

1902 GMT –– Iran ta yi ikirarin harinta na makamai masu linzami ya shafi sansanonin sojin Isra'ila 3

Rundunar juyin juya hali ta Iran ta yi ikirarin cewa an harba makamai masu linzami kan wasu wuraren sojojin Isra'ila uku a Tel Aviv, kamar yadda kafar yada labaran gwamnatin Iran ta ruwaito.

Sabbin bayanai:

Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Isra'ila ta sanar da rufe sararin samaniyar ƙasar, tana karkatar da jirage zuwa wasu filayen jiragen na ƙasashen waje a cewar kafar yada labaran Isra'ilan Sanarwar na zuwa ne bayan da Iran ta harba makamai masu linzami sama da 100 cikin Isra'ila.

Idan har gwamnatin masu tsananin aƙidar kafa ƙasar Isra'ila ta mayar da martani kan ayyukan Iran, to za ta fuskanci munanan hare-hare - in ji Dakarun kare juyin juya hali na Musulunci na Iran.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar Turkiyya Anadolu Agency ya rawaito cewa an ga makamai masu linzami da yawa a samaniyar Gabar Yammacin Kogin Jordan suna fitowa daga gabas zuwa Negev na Tel Aviv.

1636 GMT –– Iran ta harba ɗaruruwan makamai masu linzami cikin Isra’ila

Rundunar sojin Isra’ila ta ce an harba daruruwan makamai masu linzami cikin Isra’ila daga Iran.

Rundunar ta ce ana ta jin ƙarar jiniya da na hare-haren sama a fadin kasar. Kafofin yada labaran Isra'ila sun ruwaito cewa Iran ta harba makamai masu linzami sama da 100 kan Isra'ila.

An umurci mazauna birnin Tel Aviv da su nemi mafaka su kuma su kasance kusa da matsugunan da bama-bamai ba za su same su ba.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa an ji karar fashewar wasu abubuwa a Birnin Kudus.

Kamfanin dillancin labaran Iran ya rawaitoa cewa an harba makamai masu linzami cikin Isra'ila daga Iran.

Iran ta tabbatar da kaddamar da harin makami mai linzami kan Isra'ila, a cewar kafar yada labaran kasar.

1431 GMT –– Amurka ta sha alwashin kare Isra'ila, tana mai gargadin harin makami mai linzami daga Iran

Wani babban jami'in Fadar White House ya ce Amurka na matukar goyon bayan shirye-shiryen kare Isra'ila daga harin soji kai tsaye daga Iran.

Jami'in ya ce Amurka ta gano alamun cewa Iran na shirin kai harin makami mai linzami kan Isra'ila nan ba da dadewa ba.

Harin makami mai linzami da Iran ta kai wa Isra'ila na iya zama babba ko kuma mai yuwuwa fiye da wanda aka yi a watan Afrilu, idan har ya ci gaba, duk da cewa ƙimantawar ta dogara ne kan alamun farko kuma da wuya a iya tabbatarwa, kamar yadda wani jami'in Amurka ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Gargadin ya biyo bayan sanarwar da Isra'ila ta yi na cewa dakarunta na kwamandoji da dakarun sa-kai sun kaddamar da hare-hare a kudancin kasar Labanon a wani hari mai iyaka.

A halin da ake ciki, ofishin jakadancin Amurka a Isra'ila ya umurci dukkan ma'aikata da 'yan'uwansu da su nemi mafaka har sai an sanar da su.

1434 GMT –– Maldives na neman shiga shari'ar kisan kare dangi ta Afirka ta Kudu akan Isra'ila

Kasar Maldives ta ce a hukumance ta gabatar da sanarwar shiga cikin shari’ar kisan kare dangi da Agirka ta Kudu ta shigar da Isra’ila kan kisan kiyashi a Gaza a kotun kasa da kasa ta ICJ.

"Maldives, karkashin kuduri na ashirin da 63 sun gabatar da sanarwar shiga tcikin shari'ar tuhumar kisan kiyashi a Gaza (tsakanin Afrika ta Kudu da Isra'ila)," in ji Shugaban Maldives Mohamed Muizzu a cikin wata sanarwa da ya fitar a X.

1408 GMT –– Isra'ila ta kai hare-hare a Beirut, yankunan kudancin kasar, in ji majiyoyi

Isra'ila ta kai hare-hare guda biyu a Beirut, inda ta kai hari a yankunan kudancin babban birnin kasar Lebanon da kuma kofar shiga kudancin birnin, kamar yadda wasu majiyoyin tsaro biyu suka bayyana.

Majiyar ta ce an kai hari a wani babban bene a yankin Jnah na birnin.

Sojojin Isra'ila sun ce suna kai hari kan babban birnin kasar Labanon kuma sun kai wani harin da ya dace.

1315 GMT –– Erdogan ya ce za a dakatar da Isra'ila ko ba dade ko ba dade

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi Allah wadai da mamayar da Isra'ila ta yi a kasar Lebanon, sannan ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin kasa da kasa musamman su dakatar da Isra'ila ba tare da ɓata lokaci ba.

"Duk abin da za ta yi, ko ba dade ko ba jima za a dakatar da Isra'ila," in ji Erdogan ga majalisar dokokin Turkiyya a lokacin bude shekarar majalisar.

1259 GMT –– Isra'ila ta yi kira da a kwashe mutane yayin da Hezbollah ta musanta kai hare-hare ta ƙasa

Sojojin Isra'ila sun gargadi mutane da su kwashe kusan dozin biyu al'ummomin kan iyakar Lebanon sa'o'i bayan sanar da abin da ta ce takaita kutsawa ta kasa a kan kungiyar Hezbollah.

Kungiyar Hezbollah ta musanta cewa sojojin Isra'ila sun shiga kasar Lebanon, amma bayan sa'o'i sojojin Isra'ila sun sanar da cewa sun kai hare-hare da dama ta kasa a kudancin Lebanon a kusan shekara guda.

Isra'ila ta bukaci mutane da su ƙaura zuwa arewacin kogin Awali, mai tazarar kilomita 60 daga kan iyaka da kuma nesa da kogin Litani, wanda ke nuni da gefen arewa na wani yanki da Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana, wanda aka yi niyya a matsayin wani shinge tsakanin Isra'ila da Lebanon bayan yakin 2006.

1117 GMT –– Ma'aikatar Lafiya a Gaza ta ce adadin wadanda suka mutu a yakin ya kai 41,638

Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu a Gaza ta ce akalla mutane 41,638 ne suka mutu a yakin da Isra'ila ke yi a yankin da aka yi wa kawanya, wanda yanzu haka ke cikin wata na 12.

Adadin wadanda suka mutu ya hada da mutum 23 da suka mutu a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, a cewar ma'aikatar, wadda ta ce mutum 96,460 ne suka jikkata a Gaza tun lokacin da aka fara yakin a ranar 7 ga watan Oktoban bara.

TRT World