Har yanzu Hezbollah tana da tsari duk da hare-haren da Isra'ila - in ji Rasha / Photo: Reuters

Laraba, 9 ga watan Oktoba, 2024

1214 GMT — Har yanzu kungiyar Hezbollah tana da tsari duk da hare-haren Isra'ila, in ji Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar Rasha, tana mai cewa Tel Aviv tana kokarin tada rikici a Gabas ta Tsakiya.

Mai magana da yawun FM Maria Zakharova ta shaida wa manema labarai cewa, bisa ga nazari da muka yi, kungiyar Hezbollah, ciki har da reshen soji, ba ta rasa tsari na yadda take gudanar da ayyukanta ba.

Zakharova ya ce Ƙasashen Yammacin Duniya musamman Amurka da Birtaniya na rura wutar rikici a yankin Gabas ta Tsakiya tare da nuna munafunci ta hanyar goyon bayan da suke bai wa Isra'ila wanda ke janyo asarar rayukan fararen hula a Lebanon.

0553 GMT — Falasdinawa 400,000 sun maƙale a Gaza a cikin hare-haren Isra'ila - MDD

Philippe Lazzarini, Babban Kwamishinan Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijirar Falasdinu ta Majalisar Dinkin Duniya UNRWA, ya ce akalla Falasdinawa 400,000 ne suka makale a arewacin Gaza, suna fuskantar karuwar mamayar Isra’ila.

"Umarnin ficewa na baya-bayan nan daga Hukumomin Isra'ila na tilasta wa mutane sake yin gudun hijira, musamman daga sansanin Jabalia," in ji Lazzarini a wata sanarwa da ya fitar ta shafin sa na sada zumunta na X.

Mutane da yawa da iyalai da yawa sun ƙi ƙaura, suna sane da cewa babu wani wuri a cikin Gaza da ke da ingantaccen tsaro, in ji shi.

Yayin da mamayar Isra'ila ke ci gaba da tsananta, ana tilasta rufe matsugunai da ayyukan UNRWA, babban hafsan ya jaddada cewa an rufe wasu wurare a karon farko tun bayan yakin Gaza.

"Ba tare da samar da kayayyakin amfanin yau da kullun ba, yunwa ta sake yaduwa kuma tana kara tsanani. Wannan mamayar soji ta baya-bayan nan kuma tana barazana ga aiwatar da kashi na biyu na yakin rigakafin cutar shan inna ga yara," in ji Lazzarini.

0027 GMT — Isra'ila ta aiwatar da kisan kiyashi a Arewacin Gaza — Civil Defense

Sojojin Isra'ila sun aiwatar da kisan kiyashi a Arewacin Gaza a yayin hare-hare babu ƙaƙƙautawa da suke kai wa a yankin, a cewar rundunar tsaro ta farin kaya ta Palestinian Civil Defense.

"Mummunan yanayin rashin jinƙai da lardin arewaci yake ciki yana ƙara dagulewa a kowane lokaci a yayi da dakarun mamaya suke ci gaba da kai hare-hare a Beit Hanoun, Beit Lahia da Jabalia a kwana na huɗu a jere, inda suka ƙara yi wa mutane ƙawanya lamarin da ya hana su samun ruwa da abinci da magunguna," a cewar wata sanara da rundunar ta fitar.

"Dakarun mamaya sun aiwatar da kisan kiyashi kan fararen-hula, lamarin da ya kai ga shahadar gomman tare da jikkata ɗaruruwa," in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa gawawwakin mutanen suna warwatse a kan tituna domin kuwa ma'aikatan agaji sun kasa zuwa wuraren saboda dakarun Isra'ila suna kai hari kan motocin ɗaukar gawa da tawagar jami'an rundunar tsaro ta farin kaya.

Sanarwar ta ce sojojin Isra'ila sun yi "barazanar korar mutane fiye da 200,000da ke yankin da kuma waɗanda ke maƙwabtaka da Arewacin Gaza."

TRT World