Isra'ila ta kashe Falasɗinawa da dama sannan ta jikkata wasu da dama a hare-haren da ta kai Birnin Gaza. / Photo: AA

1304 GMT — Shugaban Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke kai kayan agaji ga Gaza ya bayyana cewa rabin wuraren da hukumar ke da su a yankin an lalata su tun bayan da Isra’ila ta soma yaƙi.

Philippe Lazzarini ya kuma bayyana cewa sama da mutum 500 sun rasu a hare-haren.

Shugaban Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke kula da ‘yan gudun hijira ya yi bayani a wani taron manema labarai da Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdelaty, wanda ya jaddada goyon bayan Masar ga hukumar ta UNRWA.

1030 GMT Aƙalla Falaɗinawa 40 Isra’ila ta kashe a wani hari da ta kai a sa’o’i 24 da suka gabata, wanda hakan ya kai adadin jama’ar da suka mutum a Gaza zuwa 38,197, daga ciki har da yara sama da 15,983 da mata 10,637, kamar yadda ma’aikatar ta Gaza ta bayyana.

Aƙalla wasu ƙarin Falasɗinawan 75 aka jikkata, wanda hakan ya ƙara adadin waɗanda suka jikkata zuwa 87, 903, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta bayyana.

0345 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa da dama a hare-haren da ta kai wasu gidaje a Gaza

Isra'ila ta kashe Falasɗinawa da dama a harin da ta kai ta sama a wani gida da ke arewacin Gaza, a cewar Hukumar Tsaron fararen-hula ta yankin.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce tawagarta ta gano gawawwaki bayan wani jirgin yaƙin Isra'ila ya kai hari a gidan iyalan Al Hajin da ke Jabalia.

Harin ya lalata gidan da ma wasu gidaje da ke yankin, a cewar wani ganau.

Tawagar hukumar tsaron da mazauna yankin na ci gaba da tona ɓaraguzai suna neman mutanen da gine-ginen suka danne.

Tun da farko, hukumar ta ce hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai a wasu yankunan Birnin Gaza sun yi sanadin mutuwar gomman Falasɗinawa tare da jikkata wasu da dama.

“Mutane da dama sun yi shahada, wasu sun jikkata sannan gine-gine sun danne wasu a yankunan al-Daraj, Tuffah da Tsohon City sakamakon hare-haren bamabamai na rashin hankali da sojojin mamaya suka kai waɗannan yankuna,” in ji Mahmoud Basal, mai magana da yawun hukumar, a wata sanarwa da ya fitar.

0100 GMT — An kwashe majinyata daga Asibitin Al-Ahli Baptist bayan Isra'ila ta yi gargaɗin kai hari

Ma'aikatan lafiya a Gaza sun kwashe Falasɗinawa majinyata daga Asibitin al-Ahli Baptist bayan rundunar sojin Isra'ila ta yi gargaɗi ga mutane su fice daga yankunan Al-Daraj, Al-Tuffah da Tsohon Birni da ke Birnin Gaza.

Wata majiya a asibitin da ta yi magana da kamfanin dillancin labarai na Anadolu Agency ta ce tawagar ma'aikatan kiwon lafiya ta kwashe majinyata da sauran masu ƙananan larurori daga asibitin zuwa wata cibiyar kula da lafiya da ke arewacin Gaza.

Majiyar ta ce Isra'ila ta tura jirage marasa matuƙa da yawa yankin da asibitin yake, inda suka riƙa buɗe wuta kan fararen-hula abin da ya sa ma'aikatan asibitin kwashe majinyatar.

Tun da farko, jiragen yaƙin Isra'ila da sun yi ta kai hari a wasu yankunan Birnin Gaza, inda suka jikkata gomman mutane tare da korar dubban iyalai daga gidajensu, a daidai lokacin da sojojin na Isra'ila suka umarci mutane su fita daga gidajensu.

Rundunar sojin Isra'ila ta yi gargaɗi ga mutane su fice daga yankunan Al-Daraj, Al-Tuffah da Tsohon Birni da ke Birnin Gaza . / Hoto: AFP

0130 GMT — Rundunar sojin Amurka ta ce ta lalata jirage mara matuƙa huɗu na ƙungiyar Houthi a cikin awanni 24

Cibiyar Bayar da Umarni ta Sojojin Amurka ta ce dakarunta sun lalata jirage biyu mara matuƙa na Houthi cikin awanni 24 a yankin da ke ƙarƙashin ikon Houthi a Yemen sannan ƙawayenta sun lalata jirage biyu mara matuƙa na Houthi a Gaɓar Tekun Aden.

"An tabbatar cewa waɗannan jirage suna barazana ga Amurka da dakarun haɗin-gwiwa da jiragen ruwan kasuwanci a yankin. An ɗauki wannan mataki ne domin kare 'yancin tafiye-tafiye da tabbatar da tsaron teku da ma tabbatar da tsaron Amurka da rundunar haɗin-gwiwa da jiragen ruwan kasuwanci," in ji wata sanarwa da cibiyar ta fitar.

TRT Afrika da abokan hulda