Sojojin sun kashe yaron ne a wani asibiti da ke Khan Younis. / Hoto: Reuters

1350 GMT — Netanyahu ya ce duk da mummunan kisan da ake yi wa sojojin Isra’ila za su ci gaba da yaki a Gaza

Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya lashi takobin ci gaba da yaki duk da “mummunan kisan” da ake yi wa sojojin Isra’ila.

Netanyahu ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a taron majalisar ministocinsa a birnin Tel Aviv.

“Wannan safiya ce mai tattare da wahala, bayan shafe rana ana yaki mai wahala a Gaza,” kamar yadda Netanyahu ya sanar a lokacin tattaunawa da ministocinsa a Tel Aviv.

A ranar Lahadi, rundunar sojin ta Isra’ila ta tabbatar da kashe dakarunta 14 a yayin arangama da dakarun Hamas a Zirin Gaza a sa’o’i 24 da suka gabata.

Benjamin Netanyahu ya lashi takobin ci gaba da yaki a Gaza. / Hoto: Reuters

1043 GMT — Sojojin Isra'ila sun kashe yaro dan shekara 13 a asibitin Gaza

Sojojin Isra’ila sun kashe yaro dan shekara 13 a wani asibiti da ke Khan Younis a kudancin Gaza.

“An kashe wani yaro dan shekara 13 a asibitin PRCS Al-Amal da ke Khan Younis sakamakon harbin da jirgi mara matuki na Isra’ila ya yi a cikin ginin asibitin,” kamar yadda kungiyar Red Crescent Society ta Falasdinu ta tabbatar.

A wata sanarwa ta daban, an kashe wasu Falasdinawa uku an raunata wasu a wani hari da Isra’ilan ta kai a wata unguwa da wasu ‘yan kasar Japan ke zaune a yammacin Khan Younis, kamar yadda majiyoyin kiwon lafiya suka tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

0902 GMT — An kashe sojojin Isra'ila takwas a Gaza, an ji wa shida mummunan rauni

Rundunar Sojin Isra’ila a ranar Lahadi ta tabbatar da kashe karin sojojinta takwas yayin arangama da dakarun Hamas a Zirin Gaza.

Rundunar ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar inda ta ce an kashe sojojin nata ne a ranar Lahadi.

Daga cikin wadanda aka kashe akwai Master Sgt. Nadav Issachar Farhi mai shekara 30 da Master Sgt. Eliyahu Meir Ohana mai shekara 28.

Sojojin sun ce akwai wasu guda shida kuma da aka yi wa mummunan rauni.

Adadin sojojin Isra'ila da aka kashe tun bayan soma yakin a ranar 7 ga watan Oktoba ya kai 484. / Hoto: Reuters

0130 GMT — Isra'ila tana hana aiwatar da shirin MDD na kai kayan agaji Gaza —Falasdinu

Falasdinawa sun zargi gwamnatin Isra'ila da yunkurin hana aiwatar da kudurin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2720 da ya bukaci a kai kayan agaji Gaza.

Wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Falasdinu ta fitar ta ce Isra'ila ta mayar da yankin Gaza zuwa "wata babbar makabarta ta fararen-hula."

Falasdinawa suna karbar abincin sadaka a sansanin 'yan gudun hijira na Rafah da ke kudancin Gaza ranar 23 ga watan Disamba, 2023, a yayin da ake ci gaba da fafatawa tsakanin Isra'ila da mayakan Hamas. /Hoto: AFP

Ta yi tir da hare-haren da Isra'ila take zafafa kaiwa yankin da kuma kisan kare-dangin da take yi wa Falasdinawa da "kakkausar murya".

Sanarwar ta ce Isra'ila ta matsa kaimi wurin yin luguden wuta a yankin abin da ke nuna "bijirewar da take yi wa al'ummar duniya," lamarin da ya sa “Isra'ila ta zafafa kai hare-hare a kowanne yanki daga arewaci zuwa kudancin Gaza, inda take rusa dukkan wuraren zama da kuma kai hari kan dukkan 'yan'adam a arewacin Gaza” matakin da ya kara fito da zaluncinta.

Hakan ya nuna cewa tsare-tsaren Isra'ila sun mayar da hankali wurin yunkurin hana aiwatar da kudurin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

2100 GMT — Ministocin Wajen Turkiyya da UAE sun tattauna kan halin da ake ciki a Gaza

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan da takwaransa na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sun tattauna ta wayar tarho kan halin da ake ciki a Gaza, a cewar wasu majiyoyin diflomasiyya na Turkiyya ranar Asabar.

Fidan da Sheikh Abdullah bin Zayed Al Nahyan sun tattauna kan kudurin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya game da halin da ake ciki a Gaza da kuma kai kayan agaji.

Fidan ya bayyana muhimmancin yin amfani da wannan dama wajen kai kayan agaji da kuma tabbatar da zaman lafiya ta hanyar bai wa Falasdinu kasa mai cin gashin kanta.

TRT Afrika da abokan hulda