1720 GMT — Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana cewa kare fararen hula "Dole ya zama mai muhimmanci" a yakin da ake yi tsakanin Isra'ila da Falasdin, inda ya yi gargadi kan cewa Gaza na koma wa "makabartar yara kanana."
Guterres ya shaida wa 'yan jaridu cewa "hare-hare ta kasa da sojojin Isra'ila ke kaiwa na ci gaba da ruwan bama-bamai kan fararen hula, asibitoci, sansanonin 'yan gudun hijira, masallatai, cocina da wuraren ayyukan MDD - da suka hada da gidaje. Babu wanda ya tsira,"
Ya ce karara ana aikata laifukan take hakkokin da adam da dokokin kasa da kasa, kuma yana sake kira da a tsagaita wuta don samun damar taimaka wa mutane.
1541 GMT — Hamas ta ce ta harba makaman roka 16 Isra'ila daga Labanon
Mayakan Hamas sun harba rokoki 16 daga kasar Lebanon zuwa arewacin Isra'ila, in ji reshen kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa, inda suka ce sun kai hari a kudancin birnin Haifa na gabar Tekun Isra'ila.
Rundunar ta Qassam ta ce ta kai harin ne "a matsayin martani ga kisan kiyashin da mamayar da Isra'ila ke yi da kuma kisan kiyashin da take yi kan mutanenmu a Gaza".
A hannu guda kuma rundunar sojin Isra'ila ta sanar da cewa an harba makamai masu linzami 30 arewacin Isra'ila daga kasar Lebanon, inda ta ƙara da cewa ita ma ta yi luguden wuta kan inda aka harbo su.
An sake buɗe iyakar Gaza da Masar don kwashe mutane: Hamas
An sake buɗe kan iyakar Rafah da ke tsakanin Gaza da Masar don kwashe ƴan ƙasashen waje da masu shaida zama yan ƙasa biyu da kuma Falasɗinawa da suka ji munanan raunuka daga yankin da dakarun Isra'ila ke ta yi wa ruwan wuta, kamar yadda Hamas ta ce.
An buɗe hanyar na tsawon kwana uku a makon jiya a ranakun Laraba da Alhamisa da Juma'a don fitar da Falasdinawan da suka jikkata da kuma masu ɗauke da fasfunan ƙasashen waje don su tsallaka kafin Asabar da Lahadi yayin da ake ciki wata tirka-tirka kan batun wucewar motocin ɗaukar marasa lafiya na asibiti.
Majiyoyi daga ƙungiyar Hamas sun ce an sake buɗe hanyar ne bayan wata yarjejeniya da Isra'ila — wacce aka cimma sakamakon shiga tsakanin da Masar ta yi — don a samu damar fitar da mutum 30 da suka ji raunuka.
Motocin asibiti na ɗaukar marasa lafiya shida ne suka isa kan iyakar daga ɓangaren Masar a ranar Litinin suka ɗauki Falasɗinawan da suka ji raunuka wadanda za a kai su asibitoci, kamar yadda wani jami'in kan iyaka ya shaida wa AFP.
0244 GMT — Afirka ta Kudu za ta janye dukkan jakadunta daga Isra'ila
Gwamnatin Afirka ta Kudu ta ce za ta janye dukkan jakadunta daga Isra'ila don nuna damuwarta a kan halin da ake ciki a Gaza.
Pretoria ta kuma ce matsayin jakadan Isra'ila a kasar yana kara zama "mara makama", inda ta zargi jami'in diflomasiyyar da yin kalaman ɓatanci ga mutanen da ke sukar Isra'ila.
"Gwamnatin Afirka ta Kudu ta yanke shawarar janye dukkan jami'an diflomasiyyarta da ke Tel Aviv don tuntuɓar juna," in ji Khumbudzo Ntshavheni, minista a ofishin shugaban kasar, kamar yadda ya faɗawa manema labarai a ranar Litinin ba tare da ƙarin bayani ba.
1310 GMT — China ta yi kira kan kasashen duniya su dakatar da 'bala'in' da ke faruwa a Gaza
China ta yi kira ga kasashen waje kan su fito su dakatar da Gaza da bala’in da ke faruwa a Gaza a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a Falasdinu.
Martanin na Beijing na zuwa ne bayan dakarun Isra’ila sun kai hari kan motocin daukar marasa lafiya a ranar Juma’a, kamar yadda kafar watsa labarai ta kasar ta ruwaito.
1108 GMT — Isra'ila ta ce an sake kashe mata wani soja a Gaza
Sojojin Isra’ila a ranar Litinin sun ce an sake kashe musu soja guda a Zirin Gaza a lokacin da sojojin ke ci gaba da kai hare-hare ta kasa a can.
Wata sanarwa da sojojin suka fitar ta ce sojan yana daga cikin dakarun bataliya ta tara.
Isra’ilar ta ce zuwa yanzu sojojinta 30 aka kashe sannan 260 suka samu rauni tun bayan da ta fara kai hari ta kasa a Gaza a ranar 27 ga watan Oktoba.
0830 GMT — Isra'ila ta kashe sama da mutum 200 a Gaza a cikin dare
Hare-haren Isra’ila sun kashe sama da mutum 200 a cikin dare a Gaza, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu ta tabbatar.
“Sama da mutum 200 aka bayar da rahoton sun yi shahada a kisan kiyashin da aka yi cikin dare” kamar yadda ma’aikatar ta bayyana a wata sanarwa, inda ta ce mutanen a Gaza kadai aka kashe su da arewacin Gaza.
0730 GMT — Dakarun Isra'ila sun kama 'yar gwagwarmayar Falasdinawa Ahed Tamimi
Sojojin Isra’ila a ranar Litinin sun kama daya daga cikin masu gwagwarmaya a Gabar Yamma da Kogin Jordan wato Ahed Tamimi, kamar yadda mahaifiyarta ta tabbatar.
“An kama Ahed mai shekara 23 bayan kai samame a gidanmu,” kamar yadda mahaifiyarta Nariman Tamimi ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.
Ta bayyana cewa sojojin na Isra’ila sun gudanar da bincike a cikin gidan sannan kuma suka kwace wayoyin salula na iyalan gidan.
0715 GMT — An harba rokoki daga Gaza zuwa Tel Aviv
'Yan sandan Isra'ila sun ce an harba rokoki da dama daga Gaza zuwa birnin Tel Aviv da yankunan da ke makwabtaka da shi.
Jaridar Yedioth Ahronoth ta ambato 'yan sanda suna cewa wani makamin roka ya fada a wan sarari a birnin Rishon Lezion nkusa da Tel Aviv.
Qassam Brigades, wato fannin soji na kungiyar Hamas, ya ce shi ne ya harba rokokin a Tel Aviv domin yin raddi kan kashe fararen-hula da Isra'ila ke yi a Gaza.
0600 GMT — Sarkin Jordan ya ce an wurga 'magunguna na bukatun gaggawa' a Gaza
Jiragen sojin saman Jordan sun wuwwurga magunguna da ake bukata cikin gaggawa a asibitocin tafi-da-gidanka da ke yankin Gaza da aka mamaye, a cewar Sarki Abdullah II da safiyar Litinin.
"Sojojin samanmu marasa tsoro sun jefa magunguna da ake bukata cikin gaggawa a asibitin wucin-gadi na Jordan da ke Gaza," in ji sarkin a sakon da ya wallafa a shafin X.
0534 GMT — Rundunar Sojin Ruwan Amurka ta aika da jirgin ruwan nukiliya Gabas ta Tsakiya
Rundunar Sojin Ruwan Amurka ta ce aika da jirgin ruwan nukiliya yankin Gabas ta Tsakiya.
“Ranar 5 ga watan Nuwamba, jirgin ruwa samfurin Ohio-class ya isa yankin da ke karkashi ikon Amurka,” in ji sanarwar da Cibiyar Tsare-Tsare ta Amurka (CENTCOM) ta wallafa a shafin X.
Amurka ta aika da jirage biyu yankin Gabas ta Tsakiya tun daga ranar 7 ga watan Oktoba lokacin da kungiyar Hamas ta Falasdinawa ta kaddamar da farmakin Operation Al Aqsa Flood a Isra'ila.
0400 GMT — Adadin mutanen da suka mutu a Gaza sakamakon hare-haren Isra'ila ya kai 9,770
Ma'aikatar Kiwon Lafiya a Gaza ta ce ya zuwa ranar Lahadi mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren da Isra'ila take kaiwa a Zirin Gaza sun kai 9,770.
“Mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren Isra'ila a Zirin Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba sun kai 9,770, cikinsu har da kananan yara 4,800 da mata 2,550,” in ji sanarwar da ma'aikatar ta fitar.
Ta kara da cewa a cikin awa 24 da suka wuce Isra'ila ta kashe Falasdinawa 270.