Litinin, 25 ga watan Nuwamba, 2024
2151 GMT — Wakilin Amurka Amos Hochstein ya yi barazanar janyewa daga sanya baki wajen ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Lebanon idan mahukuntan Tel Aviv ba su amince da shawarar Amurka ba, kamar yadda gidan talbijin na Isra'ila Channel 13 ya ruwaito.
Hochstein ya shaida wa jakadan Isra'ila a Amurka, Michael Herzog, cewa idan shugabanni a Tel Aviv suka ƙi yarda da shawarwarin Amurka kan yadda za a tsagaita wuta a Lebanon, Amurka za ta janye hannunta daga shiga tsakanin da take yi wajen ganin ɓangarorin biyu sun yi sulhu, a cewar tashar ta talbijin.
Ƙarin labarai👇
0009 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa biyu a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye
Sojojin Isra'ila sun kashe wani yaro Bafalasɗine tare da wani matashi a harin da suka kai a garin Ya'bad da ke kudancin birnin Jenin na Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.
Ma'aikatar kiwon lafiya ta Falasɗinu ta tabbatar da wannan labari a wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce Isra'ila ta kashe Muhammad Hamarsheh, ɗan shekara 13 da Ahmad Zaid, ɗan shekara 20.
Kamfanin dillanacin labaran Falasɗinu,WAFA, ya ruwaito cewa dakarun Isra'ila sn kutsa cikin garin Ya'bad ta gabashin garin, lamarin da ya haddasa taho-mu-gama tsakaninsu da mazauna yankin.