1400 GMT — An kashe Falasdinawa 100 a hare-haren da aka kai musu cikin dare a Gaza
Aƙalla Falasɗinawa 100 aka kashe a wasu hare-hare da aka kai cikin dare da safiyar yau Laraba a Gaza, a yayin da rundunar sojin Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare yankin da ta yi wa ƙawanya gabanin cimma yarjejeniyar da za ta fara aiki a ranar Alhamis.
Dukkan ɓangarorin sun tabbatar da wata yarjejeniya da aka cimma tsakanin Hamas da Isra'ila, da sa hannun Washington da Qatar, wadda ta taimaka wajen cimma yarjejeniyar da za ta sa a tsagaita wuta na wucin gadi a mummunan yaƙin da ya shiga mako na bakwai.
A cikin yarjejeniyar, a cikin kwana huɗu Hamas za ta saki aƙalla mutum 50 daga cikin 240 da take garkuwa da su tun lokacin da ta kai hari Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba, inda ita ma Isra'ila za ta saki Falasɗinawa fursunoni da take tsare da su.,
1350 GMT — Isra'ila ta kara kashe daya daga cikin mayakan Hezbollah
Kungiyar Hezbollah ta Lebanon a ranar Laraba ta bayyana cewa an kashe daya daga cikin mambobinta a yayin da suka yi arangama da jami’an Isra’ila a kusa da iyakar Lebanon da Isra’ila.
Sai dai kungiyar ba ta bayar da karin bayani kan yadda mamban ya mutu a lokacin arangamar ba.
A wata sanarwa ta daban, kungiyar ta Hezbollah ta bayyana cewa mayakanta sun kai hari kan wani taro na sojojin Isra’ila a harabar sansanin soji ta Raheb da al-Bayyad da ke Blida a kudancin Lebanon inda suka samu rauni.
1128 GMT — Isra'ila ta ce ranar Alhamis za a soma sakin rukunin farko na 'yan kasar da ke Gaza
Ministan Harkokin Wajen Isra’ila Eli Cohen ya bayyana cewa za a sako rukunin farko na fursunonin yakin Isra’ila da ke Gaza a ranar Alhamis.
Wannan na zuwa ne sa’o’i bayan bangarorin biyu sun sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki hudu.
Tuni Ma’aikatar Shari’a ta Isra’ila ta sanar da sunayen Falasdinawa 300 wadanda za a yi musayar fursunoni da su.
0835 GMT — Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas ya yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wuta
Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas a ranar Laraba ya yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wuta a Zirin Gaza.
“Mun jinjina wa Qatar da Masar kan kokarin da suka yi, kuma muna sabunta kiran da a dakatar da kai farmakin da Isra'ila ke kai wa al'ummar Falasdinu, da kai agajin jinkai, da samar da mafita a siyasance bisa dokokin kasa da kasa, wanda zai kawo karkashen mamaya da kuma jama’ar Falasdinu sun samu ‘yancinsu da iko,” kamar yadda ya kara da cewa.
Da safiyar Laraba ne Isra’ila da Hamas suka sanar da amincewa kan yarjejeniyar tsagaita wuta.
0730 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa shida a harin da ta kai Gabar Yamma da Kogin Jordan
An kashe Falasdinawa shida tare da raunata wasu a wani hari da Isra’ila ta kai ta sama a sansanin Tulkarim da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Isra’ila ya tabbatar.
Sojojin na Isra’ila sun kaddamar da samame a sashen kula da marasa lafiya na gaggawa na Asibitin Thabet Thabet da ke Tulkarim.
Haka kuma rahotanni sun ce an kashe wani Bafalasdine a yankin Qalqilya.
0700 GMT — Amurka da Rasha sun yi maraba da yarjejeniyar musayar fursunonin yaki ta Isra’ila da Hamas
Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana cewa ya ji dadi matuka kan cewa za a saki wasu daga cikin wadanda Hamas ke rike da su a karkashin yarjejeniyar da aka cimmawa.
Mista Biden din ya bayyana cewa an saki Amurkawa biyu wadanda aka kama a karshen watan Oktoba bayan an yi tattaunawa ta diflomasiyya mai zurfi.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha Maria Zakharova ta bayyana cewa kasarta na maraba da wannan yarjejeniya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na RIA na kasar ya ruwaito.