Litinin, 25 ga watan Nuwamba, 2024
0803 GMT — Akwai yiwuwar sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon nan da kwana biyu, kamar yadda kafar watsa labaran Isra’ila ta ruwaito.
Kafar watsa labarai na KAN ya ruwaito wata majiya ta Isra’ila na cewa Benjamin Netanyahu ya amince da batun yarjejeniyar tsagaita wuta da Lebanon wadda Amurka ke goyon baya.
Kamar yadda kafar watsa labaran ta ruwaito, Netanyahu ya amince wa jakadan Amurka Amos Hochstein ya ci gaba da aiki kan batun yarjejeniyar da Lebanon.
Majiyar ta Isra’ila ta bayyana cewa tuni aka kammala cim ma yarjejeniyar inda a halin yanzu Netanyahu ke aiki kan yadda zai fitar da sanarwar.
2151 GMT — Wakilin Amurka Amos Hochstein ya yi barazanar janyewa daga sanya baki wajen ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Lebanon idan mahukuntan Tel Aviv ba su amince da shawarar Amurka ba, kamar yadda gidan talbijin na Isra'ila Channel 13 ya ruwaito.
Hochstein ya shaida wa jakadan Isra'ila a Amurka, Michael Herzog, cewa idan shugabanni a Tel Aviv suka ƙi yarda da shawarwarin Amurka kan yadda za a tsagaita wuta a Lebanon, Amurka za ta janye hannunta daga shiga tsakanin da take yi wajen ganin ɓangarorin biyu sun yi sulhu, a cewar tashar ta talbijin.
Ƙarin labarai👇
0009 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa biyu a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye
Sojojin Isra'ila sun kashe wani yaro Bafalasɗine tare da wani matashi a harin da suka kai a garin Ya'bad da ke kudancin birnin Jenin na Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.
Ma'aikatar kiwon lafiya ta Falasɗinu ta tabbatar da wannan labari a wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce Isra'ila ta kashe Muhammad Hamarsheh, ɗan shekara 13 da Ahmad Zaid, ɗan shekara 20.
Kamfanin dillanacin labaran Falasɗinu,WAFA, ya ruwaito cewa dakarun Isra'ila sn kutsa cikin garin Ya'bad ta gabashin garin, lamarin da ya haddasa taho-mu-gama tsakaninsu da mazauna yankin.