Juyin mulki: Sojojin Faransa sun 'shirya mayar da martani' a Nijar

Juyin mulki: Sojojin Faransa sun 'shirya mayar da martani' a Nijar

Jakadan Faransa ya ki bin umarnin sojojin Nijar na fita daga kasar.
Sojojin Faransa sun ce daga yanzu ba za su yarda a sake kai wa kami'an kasarsu da ke aiki a Nijar hari ba. / Hoto: Reuters

Rundunar sojin Faransa ta ce ta shirya mayar da martani idan aka sake kai hari kan dakaru da ma'aikatan diflomasiyyarta da ke aiki a Jamhuriyar Nijar.

"A shirye rundunar sojin Faransa take ta yi raddi idan aka sake kai wa sojojinta da ma'aikatan diflomasiyyarta hari a Nijar," kamar yadda wani Hafsan sojin Faransa ya gaya wa kamfanin dillancin labarain Anadolu na kasar Turkiyya a wani rubutaccen sako ranar Juma'a.

"Sojojin suna aiki ne a kebantaccen wuri a sansanin sojin sama da ke Yamai da kuma shingayen duba ababen hawa tun ranar 26 ga watan Yuli, saboda an soke dangantakar soji tsakaninsu da Rundunar Sojin Nijar," in ji Hafsan sojin.

A makon jiya ne sojojin da suka yi wa Mohamed Bazoum juyin mulki suka bai wa jakadan Faransa da ke Nijar Sylvain Itte wa'adin 48 ya fita daga kasar.

Labari mai alaka: Sojojin Nijar sun katse lantarki da ruwa a ofishin jakadancin Faransa

Sai dai Jakada Itte ya ki bin umarnin sojojin kamar yadda Shugaba Emmanuel Macron ya bayyana.

Ranar Alhamis sojojin Nijar sun umarci 'yan sanda su fitar da jakadan Faransa daga kasar kamar yadda wata wasika daga Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar ta bayyana.

Sojojin sun ce Itte "ba zai ci gaba da samun kariya da ake bai wa jami'an diflomasiyya ba."

Nijar ta fada rikicin siyasa ranar 26 ga watan Yuli bayan Janar Abdourahamane Tiani, tsohon shugaban runduna ta musamman da ke tsaron fadar shugaban kasa, ya jagoranci kifar da gwamnatin Bazoum.

AA