1615 GMT — Isra'ila ta saki tan 40,000 na bama-bamai a cikin Gaza tun daga soma yaki
Ofishin watsa labarai na gwamnatin Gaza ya bayyana cewa sojojin Isra’ila sun ajiye tan 40,000 na bama-bamai a Gaza, tun daga 7 ga watan Oktoba.
Salama Maarouf wanda shi ne shugaban ofishin watsa labaran ne ya fitar da wata sanarwa a Telegram a rana ta uku ta yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas.
Isra’ila ta kashe dubban mutane a Gaza tun daga soma wannan yakin.
1350 — Asibiti uku kadai ke aiki a arewacin Gaza mai mutum 900,000
Wani babban jami’i a ranar Lahadi ya yi gargadi kan cewa asibiti uku kadai ke aiki a Arewacin Gaza wadanda ke kula da kusan mutum 900,000 da ke wurin.
Kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya ruwaito Munir Al-Bursh wanda shi ne Darakta Janar na Ma’aikatar Lafiya a Gaza yana cewa a halin yanzu asibitocin na daf da rufewa saboda tarin matsaloli.
Ya jaddada cewa akwai bukatar a kawo magunguna da sauran kayayyakin asibiti masu yawa domin shawo kan matsalar da ake fama da ita a halin yanzu.
1150 GMT — Isra'ila ta kashe kwamandojin Hamas hudu
Dakarun sojin Hamas na Falasdinu sun sanar da kashe kwamandojinsu hudu a Gaza, daga ciki har da Ahmad Ghandour wanda shi ne kwamandan Arewacin Gaza.
“Al Ghandour (Abu Anas) mamba ne a majalisar soji kuma kwamanda ne a Arewaci,” kamar yadda rundunar Al-Qassam ta bayyana a wata sanarwa da ta wallafa a shafin Telegram.
1100 GMT — Isra'ila ta kashe manomi a sansanin 'yan gudun hijira
Isra’ila ta kashe wani manomi da kuma ji wa wani rauni a wata gona da ke sansanin ‘yan gudun hijira ta Maghazi a Gaza.
Kungiyar bayar da agaji ta Red Crescent ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a yau Lahadi.
Wannan lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da aka shiga kwana na uku na yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma musayar fursunoni tsakanin Falasdinawa da kuma Isra’ila.
1045 GMT — Isra'ila ta kashe karin Falasdinawa biyu a Gabar Yamma da Kogin Jordan
Sojojin Isra'ila sun kara kashe Falasdinawa biyu a garuruwan Nablus da Jenin da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye, kamar yadda Ma'aikatar Lafiya ta tabbatar.
Ma'aikatar Lafiyar ta ce a cikin sa'o'i 24, akalla Falasdinawa bakwai dakarun na Isra'ila suka kashe a cikin sa'o'i 24 a daidai lokacin da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Falasdinawa ta shiga kwana na uku.
A bangare guda kuma, gidan fursunan Isra'ila ya ce ya karbi jerin sunayen Falasdinawa 39 wadanda ake sa ran saki a ranar Lahadi, kamar yadda kafar watsa labarai ta Isra'ilar ta ruwaito.