1000 GMT — Falasɗinawa aƙalla takwas ne suka mutu, cikinsu har da yara, sannan gomman sun jikkata a wani harin tsakar dare da dakarun Isra'ila suka kai sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza, a cewar majiyoyi.
Majiyoyi daga asibiti sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa an ka gawawwakin Falasɗinawan takwas, ciki har da yara, Asibitin Al-Aqsa Martyrs da ke Deir al Balah, a tsakiyar Gaza.
Dakarun Isra'ila sun yi ta luguden wuta a gabashin Deir al Balah da yankunan da ke kudu maso gabashin sansanin Bureij.
A Birnin Gaza, ganau sun shaida wa Anadolu cewa motocin yaƙi na Isra'ila sun harba bama-bamai a kusa da yankin Musalba da ke kudancin Zeitoun.
A Kudancin Gaza, sojojin Isra'ila sun yi luguden bama-bamai a gidajen da ke yammacin birnin Rafah, in ji wasu ganau a hira da Anadolu.
Hakan ya faru ne a daidai lokacin da ake fafatawa tsakanin ƙungiyar fafutukar kare Falasɗinawa da dakarun Isra'ila a yankunan da ke yammacin Rafah.
0511 GMT — Mayaƙan Houthi sun ɗauki alhakin kai hari da jirgi mara matuƙa a Tel Aviv
Ƙungiyar Houthi ta ƙasar Yemen ta ce ita ta kai hari da jirgi mara matuƙi a birnin Tel Aviv da ya jikkata aƙalla mutum 10 sannan ya kashe mutum ɗaya, a cewar hukumomi.
Kafar watsa labaran gwamnatin Isra'ila ta ruwaito cewa “wani jirgi mara matuƙi maƙare da bama-bamai ya sake su a mahaɗar ababen hawa ta Shalom Aleichem da Ben Yehuda Streets da ke Tel Aviv, ɗaruruwan mitoci daga Ofishin Jakadancin Amurka.”
Kakakin rundunar sojin Isra'ila ya ce “bama-baman sun fashe ne da sanyin safiyar Juma'a a Tel Aviv sakamakon harin da aka kawo ta sama.”
“Harin bai sa jiniya ta yi ƙara ba kuma yanzu haka ana gudanar da bincike a kansa,” in ji shi.
Wani gidan talbijin a Isra'ila Channel 13 ya ambato wani rahoton wucin-gadi na soji da ke cewa an hango jirgi mara matuƙi da ya kai hari Tel Aviv amma an gaza kakkaɓo shi sakamakon “wani kuskure na ɗan'adam,” ba tare da yin cikakken bayani ba.
An kai harin ne awanni kaɗan bayan rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da cewa ta kashe wani kwamanda da wasu mayaƙan Hezbollah a wani hari ta sama da ta kai a kudancin Lebanon.
0343 GMT — Kotun MDD za ta yanke hukunci kan mamayar da Isra'ila ta yi wa ƙasar Falasɗinu
Babbar kotun MDD za ta bayyana ra'ayinta game da abin da doka ta ce a kan mamayar da Isra'ila ta yi wa yankunan Falasɗinawa tun daga shekarar 1967, a yayin da ƙasashen duniya suke ci gaba da matsa lamba kan Isra'ila game da yaƙin da take yi a Gaza.
A gefe guda, Afirka ta Kudu ta kai ƙarar Isra'ila a gaban kotun inda ta zarge ta da kisan ƙare-dangi a Gaza.
Bai zama dole a yi biyayya ga hukuncin kotun ta ICJ ba, amma matakin nata na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da fargaba kan luguden wutar da Isra'ila take yi a Gaza.
Alƙalan kotun za su bayyana ra'ayinsu da misalin ƙarfe ɗaya na rana a agogon GMT a birnin Hague.