Asabar, 31 ga Agusta, 2024
1012 GMT — Akalla Falasdinawa 14 ne suka mutu sannan wasu da dama suka jikkata sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai a tsakiyar Gaza da kuma kudancin Gaza.
Majiyoyin lafiya a asibitin Al-Awda sun shaida wa Anadolu cewa Falasdinawa 9 ne suka mutu, yayin da wasu sama da 10 suka jikkata a wani harin da Isra'ila ta kai kan wani gida da ke yammacin sansanin Nuseirat da ke tsakiyar Gaza.
A gefe guda kuma, rundunar tsaron farar hula ta Falasdinu a Gaza ta ce an kashe Falasdinawa biyar tare da jikkata wasu 15 yayin da sojojin Isra'ila suka kai hari kan wani gida a Khan Younis da ke kudancin Gaza.
2126 GMT — Sojojin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa 12 a jerin hare-hare a yankin Gaza da aka mamaye, yayin da aka zaƙulo wasu gawawwaki daga wuraren da sojojin Isra'ila suka bari, da suka yi ka-ka-gida a baya.
Mai magana da yawun Cibiyar Kare Fararen-Hula ta Falasɗinawa Mahmoud Basal ya bayyana cewa an kashe Falasɗinawa shida a wasu hare-haren Isra'ila biyu ta sama a Jabalia da ke arewacin Gaza, ciki har da wani hari da aka kai wa wani taron mutane.
A unguwar Sheikh Radwan da ke arewa maso yammacin Birnin Gaza kuwa, an kashe wani Bafalasɗine a harin jirgin saman Isra'ila a wani gida da ake zama, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
A tsakiyar Gaza ma, an kashe Falasɗinawa biyu a wani hari ta sama kan wani gida a sansanin 'yan gudun hijira na Al-Maghazi da kuwa wani wajen da jama'a suka taru a Deir al-Balah.
A Khan Younis kuma, Falasɗinawa uku aka kashe a wani hari ta jirgin yaƙi a kan wani gida a garin Abasan al-Kabira, a gabashin Khan Younis.
2258 GMT — An jikkata Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna a Gaɓar Yamma
An jikkata aƙalla Isra'ilawa 'yan kama-wuri-zauna huɗu a wasu hare-hare daban-daban a haramtattun matsugunai na Gush Etzion a kudancin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye.
Kafofin watsa labaran Isra'ila sun ba da rahoton cewa sojojin Isra'ila sun kashe waɗanda suka kai harin.
Gidan Rediyon Sojojin Isra'ila ya ba da rahoton cewa wasu 'yan kama-wuri-zauna biyu sun ji rauni yayin da wani bam da aka sa a mota ya tashi a Gush Etzion; ɗaya ya ji rauni matsakaici, yayin da ɗayan kuma ya ji rauni kaɗan.