Isra'ila na ci gaba da kashe Falasɗinawa a Gaza a kullum waɗanda akasarinsu mata ne da yara. / Hoto: AA

1110 GMT — Akalla Falasdinawa 7 ne suka mutu kana wasu 12 suka jikkata bayan wani harin da Isra’ila ta kai kan wata makaranta da ta kasance mafaka a Gaza, in ji hukumar ba da agajin gaggawa ta birnin Gaza.

Wadanda suka mutu sun hada da wata mata da jaririnta, kamar yadda likitoci suka bayyana.

1111 GMT — Sojojin Lebanon sun faɗaɗa sansaninsu a kudancin ƙasar

Sojojin kasar Lebanon sun fara fadada sansaninsu a kudancin kasar domin tabbatar da ikon kasar da kuma tabbatar da cewa babu wani makami ba tare da tsarin doka ba, in ji Firaministan kasar.

A wata ganawa da ya yi da jakadun kasashen Larabawa da aka amince da su a Italiya, Najib Mikati ya ce: “Babban ƙalubalen shi ne dora wa Isra'ila alhakin keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma neman janye dakarunta daga yankin na Lebanon,” kamar yadda wata sanarwa daga ofishin firaministan ta bayyana.

2224 GMT — Isra'ila ta bai wa Falasɗinawa a arewacin Gaza wa'adin ficewa

Sojojin Isra'ila sun bai wa Falasdinawa wa'adi ba bisa ka'ida ba a kudu maso gabashin Jabalia kan su fice daga yankunan domin shirin sake kai hari.

Mai magana da yawun sojojin Avichay Adraee ya ce sun bayar da wa'adin ne saboda harin da Isra'ila ke shirin kaiwa kan wani yanki da ya ce an harba rokoki daga Isra'ila.

Ya gargadi mazauna garin da su fice zuwa "matsuguni a tsakiyar birnin Gaza."

TRT Afrika da abokan hulda