Ambulance Gaza

1511 GMT — Isra’ila ta kai hari kan motocin asibiti a kusa da Asibitin Al Shifa na Gaza

Hukumomi a Gaza sun ce Isra’ila ta kai wani harin sama kan motocin asibiti inda mutane da dama suka mutu, a cewar Ma’aikatar Lafiya ta Falasɗinu.

Wata sanarwar gwamnati ta ce dakarun isra’ila sun kai hari “kan wani jerin gwanon motocin asibiti da ke ɗauke da wasu mutanen da suka jikkata a wani harin daban,” yayin da ma’aikatar lafiyar ta ce mutane da dama sun mutu a sakamakon harin saman da ya faru a kusa da Asibitin Al Shifa a birnin Gaza.

0819 GMT Mutum 21 sun jikkata bayan harin Isra'ila a kusa da wani asibiti a Gaza

Aƙalla mutum 21 ne suka jikkata a wani harin sama na Isra'ila da aka kai kusa da Asibitin Ƙudus, a cewar Ƙungiyar Red Crescent ta Falasɗinu.

Ƙungiyar ta ce mutum 21 din sun ji raunukan ne sakamakon fashewar gilasai da faɗuwar rufi a kansu.

Mafi yawan waɗanda suka ji raunin mata da yara ne, in ji Red Crescent, tana mai cewa harin ya jawo "matsanancin tsoro da fargaba a tsakanin fararen hular da ke neman mafaka a wajen."

0722 GMT Sojin Isra'ila 24 ne suka mutu kawo yanzu bayan kashe hudu a ba-ta-kashin da aka yi a Gaza da daddare

Rundunar sojin Isra'ila ta sanar da cewa an sake kashe sojojinta huɗu a wani gumurzu da aka yi tsakaninsu da mayaƙan Falasɗinu.

A cewar Jaridar Haaretz, rundunar sojin Isra'ila ta ce dakaru 23 aka kashe mata tun farkon harin ƙasan da ta fara kai wa Gaza a ranar Talata.

Rundunar Al Qassam ta Hamas ta ce yawan Isra'ilawan da suka mutu a Gaza sun fi wanda Isra'ila ta sanar.

0429 GMT — UAE ta yi gargadi game da watsuwar rikicin Gaza

Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi gargadi cewa akwai yiwuwar watsuwar rikici a yankin Gabas ta Tsakiya sakamakon hare-haren da Isa'ila take ci gaba da kaiwa a Gaza.

Ta ce tana aiki "babu dare babu rana" domin ganin an tsagaita wuta.

"A yayin da muke ci gaba da aiki domin dakatar da wannan yaki, dole mu sani cewa akwai tasiri mai girma da zai yi a yankin idan ya kai matukar tukewa," a cewar Noura al Kaabi, karamin ministan harkokin waje, a taron da aka gudanar a brnin Abu Dhabi.

"Barazanar watsuwar yakin yankin ta hakika ce, sannan akwai yiwuwar masu tsattsauran ra'ayi su yi amfani da wannan dama wajen watsa manufofinsu da za su sa a yi ta rikici."

0428 GMT — Thailand na tattaunawa da Iran da wasu kasashe kan kubutar da ‘ya'yanta da Hamas ta yi garkuwa da su

Thailand tana tattaunawa da Iran da wasu kasashe wadanda za su tuntubi Hamas don ganin an sako mata gomman 'yan kasarta da kungiyar ta yi garkuwa da su, a cewar Ministan Harkokin Wajen kasar.

Ministan Harkokin Wajen kasar Parnpree Bahiddha-Nukara ya ce Iran, wacce ke da kusanci da Hamas, ta yi alkawarin taimakawa.

‘Yan Thailand 23 suke hannun Hamas daga cikin mutane sama da 240 da ta yi garkuwa da su a lokacin da kungiyar ta kai wa Isra’ila hari a ranar 7 ga watan Oktoba

0800 GMT — Marasa lafiya sun soma mutuwa yayin da asibiti daya tilo na cutar kansa a Gaza ya daina aiki

Marasa lafiya hudu sun mutu bayan asibitin Turkish-Palestinian Friendship, wanda shi ne daya tilo da ke kula da masu dauke da cutar kansa a Gaza, ya daina aiki.

"Mutum hudu da ke fama da cutar daji sun mutu yau bayan Asibitin Turkish-Palestinian Friendship ya daina aiki saboda rashin fetur," a cewar daraktan asibitin, Subhi Skaik, a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Anadolu Agency.

Ya kara da cewa: "Mutanen sun mutu ne sakamakon rashin isassun kayan aiki na asibiti."

A cewarsa, an dauke dukkan masu fama da cutar kansa daga asibitin zuwa Asibitin Dar al Salam da ke Khan Yunis a kudancin Gaza.

Wani Bafalasdine cikin alhini yana rike da gawar dansa da ya dauko daga mutuware na Asibitin Nasser da ke Khan Yunis, Gaza bayan Isra'ila ta kashe shi ranar 2 ga watan Nuwamba, 2023. /Hoto: AA

0734 GMT — Masar za ta kwashe mutum 7,000 daga Gaza

Ma'aikatar Harkokin Wajen Masar ta ce za ta taimaka wurin kwashe "kusan mutum 7,000" 'yan asalin Gaza wadanda kuma suke da fasfo na wasu kasashen.

Ma'aikatar Lafiyar Masar ta ce ranar Alhamis an kai Falasdinawa 21 da suka ji raunuka asibitocin Masar, sannan " mutum 344 'yan kasashen waje, da suka hada da kananan yara 72," sun wuce ta maketarar Rafah.

Wannan ne karo na biyu da Masar ta bude maketarar Rafah domin mutanen da suke fitowa daga Gaza su wuce.

A yayin taro da jakadun kasashen waje, mataimakin ministan harkokin wajen Masarr Ismail Khairat ya ce kasarsa tana shirin "kwashe 'yan kasashen waje daga Gaza ta maketarar Rafah," in ji sanarwar.

Hukumomi a Gaza sun ce Isra'ila ta kashe Falasdinawa sama da 9,000 a hare-haren da ta kaddamar daga ranar 7 ga watan Oktoban 2023. Hoto: Reuters
AA
TRT World
AFP
Reuters