Amir Abdollahian ya kuma soki Amurka, wacce ɓaro-ɓaro ta nuna goyon bayanta ga Isra'ila / Hoto: Reuters / Photo: AFP

1730 GMT — Jami'an MDD sun ce harin roka ya shafi hedikwatarsu a Labanon

Shirin Wanzar da Zaman Lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Labanon ya ce wani harin roka da aka kai ya shafi hedikwatarsu a garin Naqoura da ke kudancin kasar, a yayin da ake musayar wuta a kan iyakar ƙasar da Isra'ila.

"An kai wa hedikwatarmu da ke Naqoura harin roka kuma muna ƙoƙarin gano ko daga in ane. Ma'aikatanmu ba sa cikin ginin lokacin da abin ya faru, An yi sa'a ba wanda ya ji rauni," UNIFIL ta fada a wata sanarwa.

1700 GMT — 'Iran ba za ta ci gaba da zama 'yar kallo ba'

A wani labarin daban Firaministan Iran ya ce ƙasarsa ba za ta ci gaba da zama 'yar kallo ba a wannan lamarin na yaƙin Isra'ila da Falasdinu, kuma tuni ta gaya wa Isra'ilan ta wajen ƙawayenta cewa "idan ta ci gaba da aikata miyagun laifuka a Gaza, to za ta ga abin da zai faru ba da daɗewa ba.

1630 GMT — Iran ta yi gargaɗin lalacewar lamarin da ba za a shawo kansa ba in Isra'ila ta kutsa Gaza

Iran ta yi gargadin cewa "babu wanda zai iya ba da tabbas" kan shawo kan al'amura idan har Isra'ila ta kutsa Gaza, gabanin hare-haren da ake sa ran dakarun Isra'ilan za su kai.

"Idan har gwamnatin masu aƙidar Yahudanci ta Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare kan al'ummar Gaza, to babu wanda zai iya ba da tabbacin cewa za a iya shawo kan lamarin idan al'amura suka dagule," in ji Ministan Harkokin Wajen Iran, Hossein Amir Abdollahian lokacin da yake ganawa da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, yayin da dakarun Isra'ila ke ci gaba da mamaye kan iyaka.

"Ya kamata masu son kare ta'azzarar rikicin su dakatar da wadannan munanan hare-hare... da ake kai wa kan fararen hula a Gaza," ya ƙara da cewa.

Amir Abdollahian ya kuma soki Amurka, wacce ɓaro-ɓaro ta nuna goyon bayanta ga Isra'ila tun bayan hare-haren na ranar 7 ga watan Oktoba.

1605 GMT Kungiyar Hamas ta sake kai sabon hari birnin Ashkelon na Isra’ila

Kungiyar Hamas ta sanar da kai sabon hari birnin Ashkelon na Isra’ila domin mayar da martani kan hare-haren da Isra’ila ke kai wa Falasdinawa.

Wasu hotuna da bidiyo wadanda aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda harin ya lalata wasu gine-gine a birnin na Ashkelon da Isra’ila ta mamaye.

Wannan harin na zuwa ne a daidai lokacin da Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa adadin mutanen da suka rasu sakamakon hare-haren Isra’ila sun kai 2,450.

1523 GMT — Hezbollah ta kai hari wurare biyar na Isra'ila

Kungiyar Hezbollah ta Lebanon ta bayyana cewa ta kai hari a wurare biyar na Isra’ila

Kungiyar ta bayyana cewa wuraren biyar na kan iyakar Isra'ila da Lebanon.

Tun bayan da aka soma yaki tsakanin Isra’ila da Hamas, kungiyar ta Hezbollah ta ce a shirye take domin ta hada kai da Hamas domin yakar Isra’ila.

Ko a jiya Asabar sai da kungiyar ta Hezbollah ta harba makami mai linzami a yankunan Shebaa da Kafr Shuba da ke kudancin Lebanon wadanda Isra’ila ta mamaye.

1420 — Isra'ila ta mayar da ruwan famfo kudancin Gaza

Rahotanni daga kudancin Gaza na cewa Isra’ila ta mayar da ruwan famfo ga kudancin Gaza bayan Isra’ilar ta dauke shi na tsawon kwanaki.

Babban mai ba shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro Jake Sullivan shi ya tabbatar da hakan a wata tattaunawa da kafar watsa labarai ta CNN inda ya ce hukumomin Isra’ila ne suka tabbatar masa da hakan.

A makon da ya gabata ne sojojin na Isra’ila suka sanar da yi wa Gaza kawanya tare da katse wuta da ruwa da kuma toshe hanyar samun abinci.

1217 — Fafaroma Francis na son a agazawa jama'ar Gaza

Fafaroma Francis ya yi kira da a bayar da dama domin kai kayayyakin agaji da gudanar da ayyukan jin-kai a Zirin Gaza wanda Isra’ila ke kai wa hari.

"Dole ne a mutunta dokokin bil'adama, musamman a Gaza, sakamakon ya zama lamari na gaggawa kuma ya zama dole don tabbatar da hanyoyin jin-kai da taimakon jama'a,” kamar yadda fafaroman ya bayyana.

Ana ta nuna damuwa a fadin duniya sakamakon halin matsi da aka shiga a Gaza bayan Isra’ila ta yanke ruwa da wuta da kuma hanyoyin kai abinci, inda ta sha alwashin mamaye birnin har sai an saki Isra’ilawan da kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su.

A cikin kwanaki takwas tun bayan da ‘yan bindigan Hamas suka kashe sama da Isra’ilawa 1,300, Isra’ilar ta yi ta mayar da martani ta hanyar harba rokoki da makamai masu linzami cikin Gaza inda har mutum 2,300 suka mutu.

1016 — Isra'ila ta ce ta kashe daya daga cikin kwamandojin Hamas Bilal Al-Qudra

Sojojin Isra’ila sun bayyana cewa sun kashe daya daga cikin kwamandojin Hamas da ke da hannu a harin da aka kai wa Isra’ilar a ranar 7 ga watan Oktoba.

A wata sanarwa da ta fitar, sojojin na Isra’ila sun yi ikirarin cewa jiragensu na yaki sun kashe Bilal Al-Qudra a Zirin Gaza jiya da dare.

Sai dai Kungiyar Hamas a nata bangaren ba ta ce komai ba dangane da ikirarin da Isra’ilar ta yi.

0945 GMT — Amurka za ta soma kwashe 'yan kasarta daga Isra'ila daga gobe

Rundunar sojin Amurka ta shirya jirgin ruwa wanda zai fitar da ‘yan kasarta daga Isra’ila zuwa Cyprus a ranar Litinin.

Ofishin jakadancin Amurka da ke Isra’ila ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi inda ya ce jirgin ruwan zai bar Isra’ila ne daga tashar ruwa ta Haifa.

Ofishin jakadancin bai bayyana adadin Amurkawan da za a kwasa a cikin jirgin ba amma ya tabbatar da cewa jirgin zai soma dibar fasinjoji tun daga takwas na safe.

Akwai dubban Amurkawa da ke zaune a Isra’ila kuma tuni aka tabbatar da cewa Amurkawa 29 sun mutu a hare-haren da Hamas ta kai wa Isra’ila.

Akwai kuma wasu karin 15 da ba a gani ba inda ake zaton suna daga cikin wadanda Hamas ta yi garkuwa da su.

0730 GMT — Adadin sojojin Isra'ila da aka kashe a yakin Gaza ya kai 286

Rundunar sojin Isra'ila ranar Lahadi ta ce adadin sojinta da aka kashe bayan kaddamar da yaki da kungiyar Hamas ta Falasdinawa ya kai 286.

A cewar shafin intanet na jaridar Times of Israel , rundunar sojin Isra'ila ta bayyana sunayen sojoji bakwai da aka kashe a cikin mako guda.

Kusan kullum, rundunar sojin Isra'ila tana fitar da sunayen sabbin jami'anta da aka kashe a yakin da take yi da Falasdinawa a Gaza.

Sabbin alkaluma sun nuna cewa, Isra'ilawan da suka mutu a yakin kawo yanzu sun kai 1,300 yayin da aka tabbatar da jikkatar Isra'ilawa fiye da 3,400.

0626 GMT — Adadin Falasdinawan da Isra'ila ta kashe ya kai 2,329

Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Gaza ta ce ya zuwa ranar Lahadi Falasdinawan da Isra'ila ta kashe sakamakon hare-haren da take kai wa ta sama sun kai 2,329.

A sanarwar da ta fitar dazun nan, ma'aikatar ta kara da cewa mutanen da suka jikkata sun karu zuwa 9,042.

Hakan na faruwa ne a yayin da Isra'ila ta ce tana shirin kaddamar da hare-hare ta kasa da ta ruwa da kuma ta sama a Zirin Gaza, bayan ta bai wa mazauna arewacin Gaza wa'adin awa 24 su fice daga yankin zuwa kudancin.

A sanarwar da ta fitar dazun nan, ma'aikatar ta kara da cewa mutanen da suka jikkata sun karu zuwa 9,042./Hoto:AA

0600 GMT — Iran ta ce yakin Isra'la a Gaza zai iya haifar da 'sakamako mai tarin yawa'

Iran ta yi gargadin cewa idan Isra'ila ba ta dakatar da "laifukan yaki da kisan kare-dangi" da take yi a Gaza ba nan-take, "lamarin zai iya kazancewa kuma zai haifar da sakamako mai tarin yawa," kamar yadda ofishin jakadancin Tehran a Majalisar Dinkin Duniya da ke New York ya bayyana a shafin X, wanda a baya ake kira Twitter.

"Idan ba a dakatar da laifukan yaki da kisan kare-dangi da Isra'ila take yi nan-take ba, lamarin zai kazance kuma zai haddasa sakamako mai dimbin yawa — nauyin hakan zai rataya a wuyan Majalisar Dinkin Duniya (MDD), da Kwamitin Tsaro da kuma kwamitin gudanarwa," in ji Iran.

0522 GMT — An tabbatar da kashe Amurkawa 29 a yakin Isra'ila da Hamas

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ranar Lahadi ta tabbatar da kisan Amurkawa 29 a harin da kungiyar Hamas ta kai wa Isra'ila.

A cewar shafin intanet na kafar watsa labaran Axios, Amurka tana sane cewa ba a ga 'yan kasarta15 da kuma mutum daya da ke da izinin zama dan kasa na dindindin ba kuma tana "aiki ba dare ba rana" domin gano inda suke.

Kakakin ma'aikatar harkoki wajen Amurka yana hada gwiwa da gwamnatin Isra'ila game da wadanda aka yi garkuwa da su, ciki har da musayar da bayanan sirri.

Har yanzu ba a san adadin fursunonin Isra'ila da ke hannun Hamas ba, ciki har da 'yan kasashen waje, wadanda yanzu suke tsare a Gaza.

AA
TRT World