Ana zargin Johan Floderus da leƙen asiri a Iran. / Hoto: Reuters

Wani mai shigar da ƙara a Iran ya yi kira kan a yanke hukuncin kisa kan wani jami’in diflomasiyya na Tarayyar Turai ɗan ƙasar Sweden kan zargin leƙen asiri.

An kammala shari’ar da ake yi kan Johan Floderus ɗan shekara 33 a ranar Lahadi.

A lokacin yarjejeniyar da aka yi ta ƙarshe, mai shigar da ƙarar ya zargi ɗan ƙasar na Sweden da “haɗa kai da gwamnatin Yahudawa domin leƙen asiri,” kamar yadda jaridar Mizan Online ta ruwaito.

Mai shigar da ƙarar ya kuma yi iƙirarin cewa Floderus na da laifin “cin hanci da rashawa a doron ƙasa” wanda hakan ya sa ake buƙatar a yi masa hukunci mafi tsauri da Iran ta tanada wanda shi ne kisa.

A halin yanzu Floderus da lauyansa na da mako guda kacal su mayar da martani kan buƙatar yanke hukuncin kisan.

A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar, ta bayyana cewa mataimakin jakadan ƙasar Sweden na wurin a lokacin da aka ci gaba da shari’ar Floderus a ranar Litinin.

Ofishin jakadancin na ci gaba da aiki tare da lauyan nasa sannan suna sa ido kan lamarin.

Haka kuma sanarwar ta ce ma’aikatar na tattaunawa lokaci bayan lokaci da iyalansa. “Babu wani dalili koma mene ne na ci gaba da tsare Floderus, ballantana ma gurfanar da shi a gaban kotu.

Duka Sweden da Tarayyar Turai sun gabatar da hakan a bayyane ga wakilan Iran,” in ji ta.

Ministan Harkokin Wajen Sweden, Tobias Billstrom ya ce “za mu yi magana idan an sanar da hukuncin,” kamar yadda Anna Erhart ta bayyana, wadda ita ce sakatariyar watsa labaransa a tattaunawarta da Anadolu.

AA
Muna amfani da ka’idojin yanar gizo. Muna son ku san cewa idan kuka ci gaba da amfani da wannan shafin, kun amince da wadannan ka’idojin.Ka’idoji
Na amince