Kasar Iran ta harba wani kumbo da aka ƙera domin ɗaukar ɗan'adam da duk wani abu mai rai, a wani mataki na tura 'yan sama jannati zuwa sararin samaniya, kamar yadda kafafen watsa labaran ƙasar suka ruwaito.
Ƙasashen Yamma sun soki wannan gwajin fasahar na sararin samaniya na baya-bayan nan.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar IRNA ya ambato Ministan Sadarwa na ƙasar Issa Zarepour, yana cewa "An yi nasarar aika kumbon har tsawon kilomita 130 (mil 80).
Ya ce harba kumbon mai nauyin kilogiram 500 kan wani sabon nau'in roka da aka ƙera a cikin ƙasar mai suna “Salman” na iya bai wa ɗan'adam damar yin zirga-zirga a sararin samaniya.
Ba a dai tabbatar da ko akwai dabbobi masu rai a cikin kumbon ba, wanda harba shi ya zo ne shekara 13 bayan Iran ta aika da kunkuru da ɓera da tsutsotsi zuwa sararin samaniya.
Amurka ta yi jan hankali
Tehran ta sha fama da gazawar harba tauraron ɗan'adam da dama a baya, kuma nasarar harba tauraron ɗan'adam na farko na soja zuwa sararin samaniya a watan Afrilun 2020 ya jawo kakkausar tsawatarwa daga Amurka.
A cikin watan Satumban bana, dakarun Juyin juya halin Musulunci, ɓangaren aƙidar sojojin Iran, sun harba wani sabon tauraron ɗa' adam na soji zuwa sararin samaniya.
Iran dai ta sha musanta duk wani buri na ƙera makaman ƙare dangi, tana mai dagewa cewa tauraron ɗan'adam ɗinta da makaman harba rokokin nata na kare kai ne kawai.
Tehran dai na fuskantar tsauraran takunkuman da Amurka ta ƙaƙaba mata tun bayan ficewar Washington daga yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekarar 2018
Yarjejeniyar, wacce aka fi sani da Joint Comprehensive Plan of Action ko JCPOA, ta bai wa ƙasar sassaucin takunkumin da aka ƙaƙaba mata domin daƙile ayyukanta na nukiliya da ke da nufin hana ƙasar bunƙasa makaman nukiliya.