Lahadi, 8 ga September 2024
1316 GMT — Ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon a ranar Lahadi ta ce ta kai hari arewacin Isra’ila domin mayar da martani dangane da hare-hare ta sama da ƙasar ta kai a kudancin Lebanon.
Ƙungiyar ta ce ta harba rokoki a haramtattun matsagunan Isra’ila da ke Kiryat da Shmona da Shamir a arewacin Isra’ila domin mayar da martani dangane da harin da ƙasar ta kai a birnin Froun, wanda ya yi sanadin mutuwar jami’an kare farar hula uku da jikkata biyu.
Haka kuma ƙungiyar ta Lebanon ta ce ta kai hari kan kayayyakin sa ido na Isra’ila a Malikiya ta hanyar amfani da jirgi maras matuƙi.
0914 GMT — Sojojin Isra’ila sun kashe mataimakin shugaba Hukumar Kare Farar Hula ta Gaza a wani harin sama da suka kai.
Hukumar ce ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi inda ta ce zuwa yanzu Isra’ila ta kashe jami’anta 83 tun daga 7 ga watan Oktoba bayan soma yaƙi.
A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Mahmoud Bassal ya fitar, ya yi ta’aziyya game da “kisan da aka yi wa Mohammad Abdelhay Morsi, mataimakin daraktan hukumar kare farar hula a arewacin Gaza, wanda Isra’ila ta kashe a wani hari ta sama a gidansa da safiyar nan a yankin Al-Alami da ke Jabalia.”
Bassal ya ce baya ga jami’ansu 83 da Isra’ilar ta kashe, akwai fiye da 200 da ta jikkata.
0140 GMT — Ƙungiyar Houthi ta Yamen ta sanar da cewa ta harbo wani jirgin Amurka mara matuƙi da ke "kai hare-hare" a tsakiyar Yamen.
Mai magana da yawun dakarun Houthi Yahya Sarea ya ce tsaron Yemen na sama "ya samu nasarar" kakkaɓo jirgin Amurka mara matuƙi MQ-9 a sararin samaniyar Marib.
Sarea ya tabbatar da cewa dakarun Houthi sun ci gaba da sauke nauyinsu "na goyon bayan wahalar da Falasaɗinawa suke sha da kuma tsare Yamen."
A wani ɓangare na jaddada goyon baya ga Gaza, wanda ke fuskantar munanan hare-haren da Isra'ila ke kai wa tun daga 7 ga Oktoba, 'yan Houthi sun ringa kai hare-hare da makamai masu linzami da da jirage masara matuƙa kan jiragen ruwan Isra'ila ko waɗanda ke da alaƙa da Isra'ila da ke bi ta Bahrul Aswad, da Bahar Maliya da Tekun India,
Tun daga farkon 2024, wani ƙawance da Amurka ke jagoranta ya ringa kai hare-hare ta sama suna da'awar kai wa wuraren da 'yan Huti suke hare-hare a Yemen a matsayin martani ga hare-haren teku, waɗanda a wasu lokutan 'yan Houthi suke mayar da martani.