Israel Hezbollah / Photo: AP

1320 GMT — Hezbollah da Isra'ila sun yi musayar wuta yayin da ake fuskantar tashin hankali a kan iyaka

Kungiyar Hizbullah ta Lebanon da Isra'ila sun yi musayar wuta a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashin hankali a kan iyakar Lebanon da Isra'ila.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hezbollah ta ce ta kai hari kan wata na'urar radar a kudancin Lebanon da "makaman da suka dace", wanda kuma ya samu inda ake so "kai tsaye."

A nata bangaren, rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hare-hare a wurare da dama a kudancin kasar Lebanon, a matsayin martani ga hare-haren da kungiyar Hizbullah ta kai kan wuraren sojin Isra'ila.

Rundunar ta ce ta gano wasu makamai masu linzami da aka harba daga Lebanon zuwa wani sansanin soji da ke kusa da kauyen Arab al Aramshe da ke yammacin Galili da kuma wani shingen tsaro a yankin Hermon.

0910 GMT — An kai gawawwaki 73 da masu rauni 123 asibitin Al-Aqsa

Ma’aikatar Lafiya da ke Gaza ta tabbatar da cewa an kai gawawwakin mutum 73 da kuma mutum 123 wadanda suka samu rauni asibitin Al-Aqsa a sa’o’i 24 da suka gabata.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a fadin Falasdinu ba kakkautawa.

Kasashen duniya da dama na ci gaba da Allah wadai da kan kisan da Isra’ila ke yi a Gaza.

0147 GMT — Isra'ila za ta ci gaba da kula da tsaron Gaza bayan yaki - Netanyahu

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce sojojin ƙasarsa za su ci gaba da kula da tsaron yankin Gaza da aka yi wa ƙawanya bayan yaƙin, yana mai watsi da yiwuwar bai wa dakarun ƙasa da ƙasa wannan alhakin.

Da yake magana a wani taron manema labarai bayan ganawarsa da majalisar ministocinsa ta yaƙi, Netanyahu ya ce "dole ne a kawar da dukkan dakarun da ke Gaza" bayan kawo ƙarshen yaƙin.

Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare tun bayan kawo karshen yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimmawa tsakanin Hamas da Isra'ila. / Hoto: Reuters

"Kuma runduna ɗaya ce kawai da za ta iya ganin da aikin kawar da dakarun da ke Gazam - kuma wannan rundunar ita ce IDF," in ji shi, wato yana nufin sojojin Isra'ila, ya ƙara da cewa "babu wata rundunar ƙasa da ƙasa da za ta iya ɗaukar alhakin hakan."

"Mun ga abin da ya faru a wasu wuraren da suka kawo sojojin ƙasa da ƙasa da nufin kawar da makamai, ban shirya rufe ido don yarda da wani tsari ba."

Yayin da yake lura da cewa sojojin Isra'ila sun faɗaɗa ayyukansu zuwa kudancin Gaza da aka yi wa ƙawanya, Netanyahu ya ce sojojin sun kuma yi wa Jabalia da Khan Younis ƙawanya, yana mai cewa: "Babu wani wuri da ba za mu iya kaiwa ba."

Ya yi kira ga fararen hula da su bar yankunan da ƙasarsa ke fafatawa da kungiyar Hamas ta Falasdinu.

"A nan ina shaida wa abokanmu na duniya da ke matsa lamba don kawo ƙarshen yaƙin: Hanyarmu ɗaya tilo ta kawo ƙarshen yaƙin, da kuma kawo ƙarshensa cikin sauri, ita ce murƙushe Hamas - da kuma lalata ta," in ji shi.

1247 GMT — Iyalai a Gaza suna gudu zuwa kudancin yankin da ke cunkushe yayin da Isra'ila ke ruwan makamai masu linzami

Iyalai a Gaza sun tattara kayansu suna gudu saboda tsoron kar ruwan bama-baman da Isra'ila ke yi ya hallaka su, inda suke tafiya yankin kudancin Gaza da tuni ya cika maƙil da jama'a, sannan babu isasshen abinci da ruwa da banɗakuna.

Wasu a ranar Talata sun yi gudun hijira a karo na uku ko na hudu cikin kasa da watanni biyu.

Galibin mutanen Gaza miliyan 2.3 sun zama marasa matsugunai a yaƙin da Isra'ila ke yi a yankin na Falasdinu, lamarin da ya jawo sabon yanayin gudun hijira tun bayan da aka kawo ƙarshen tsagaita wuta na tsawon mako guda a ranar 1 ga watan Disamba, tare da ƙara taɓarɓarar da halin da ake ciki na jinƙai.

A garin Khan Younis da ke kudancin Gaza, inda Isra'ila ke ci gaba da kai farmakin da aka daɗe ana jira, Falasdinawa da suka nemi kariya daga hare-hare ta sama ta hanyar yin sansani a harabar Asibitin Nasser na birnin suna naɗe tantunansu tare da loda tabarmai da bargunansu a cikin motoci ko kekunan jakuna.

"Muna shirye-shiryen barin Khan Younis mu nufi Rafah, kusan kwanaki 50 kenan muna nan," in ji Abu Omar, wani matashin magidanci da ya bar gidansa da ke a gabashin yankin, yana samun mafaka a sansanin asibitin tare da iyalinsa.

TRT Afrika da abokan hulda