Harin da Isra'ila ta kai a sansanin Rafah ya kashe mutane 18 tare da jikkata da dama: Likitoci / Hoto: AFP / Photo: AA

1430 GMT — Harin da Isra'ila ta kai a sansanin Rafah ya kashe mutane 18 tare da jikkata da dama: Likitoci

Akalla Falasdinawa 18 ne suka mutu yayin da 35 suka jikkata bayan da sojojin Isra'ila suka harba bama-bamai a tantunan 'yan gudun hijira a yankin Mawasi da ke yammacin Rafah a kudancin Gaza.

Isra'ila ta ayyana yankin a matsayin yanki mai aminci.

Majiyoyin lafiya sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa, jami'an ceto na ci gaba da zakulo gawarwakin mutanen da suka jikkata tare da ba da kulawa ga wasu mutane masu yawa da suka jikkata bayan da tankokin Isra'ila suka kai hari kan sansanin 'yan gudun hijira da ke yankin Mawasi.

Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta yi nuni da cewa, tawagogin likitocinta na gudanar da ayyukan da suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama sakamakon harin da Isra'ila ta kai a yankin.

0650 GMT — An kashe karin sojojin Isra’ila biyu a yakin tsakiyar Gaza

Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da cewa an kashe karin sojinta biyu yayin wani yaki a tsakiyar Gaza.

A wata sanarwa, sojin sun ayyana sunayen sojoji da aka kashe, Manjo Omer Smadga, mai shekaru 25, da Manjo Janar Saadia Yaakov Dery, mai shekaru 27.

Rundunar sojin ta ce akalla sojoji biyar ne suka samu rauni, uku daga ciki mummunan rauni.

Alkaluman sojin Isra’ila sun nuna cewa akalla sojoji 664 sun rasa rayukansu, yayin da 3,871 suka samu rauni tun bayan barkewar yaki kan Gaza ranar 7 ga Oktoba, 2023.

0717 GMT — Harin sama na Isra'ila ya kashe Falasdinawa da dama a Kudancin Gaza

Kamfanin dillancin labaran Wafa ya bayar da rahoton cewa, akalla Falasdinawa uku ne suka mutu sakamakon wani hari da jiragen yakin Isra'ila suka kai a garin Khan Younis da ke Kudancin Gaza.

An kashe Yassin Muhammad al-Amour, Mahmoud Adel al-Najjar, da ɗansa Adel a harin da aka kai a garin al Fukhari.

An kuma jikkata wasu da dama a hare-haren da Isra'ila ta kai kan wasu gidaje biyu a unguwar Tuffah da al Shujaiya.

Sojojin Isra'ila sun kuma yi luguden wuta a unguwar Zeitoun, da arewacin sansanin Nuseirat, da wasu yankuna na Deir al Balah, da garin Al-Masdar, da kuma sansanin Maghazi.

0300 GMT — Amurka ta nemi Isra’ila ta kauce wa ta’azzara yaki da Hezbollah ta Lebanon

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya fada wa jami’an Isra’ila muhimmancin kauce wa ƙarin dagulewar fada da Lebanon da kuma Hezbollah.

Amurka ta nemi Isra’ila ta kauce wa ta’azzara yaki da Hezbollah ta Lebanon  

Blinken ya gana da Babban Mashawarcin Tsaro na Isra’ila, Tzachi Hanegbi da Ministan Muhimman Harkoki, Ron Dermer, a cewar Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka cikin wata sanarwa.

Da yake jaddada "cikakken goyon bayan" Amurka kan tsaron isra’ila, Blinken ya ayyana yunkurin da ke gudana don cim ma tsagaita wuta a Gaza, da samun a sako da wadanda aka yi garkuwa da su.

Sanarwar ta kara da cewa, "Sakataren ya jaddada bukatar daukar karin matakai don habaka kai kayan agaji zuwa cikin Gaza, da kuma shirin gudanar da Gaza bayan yaki, da tsaro da sake gina yankin".

2330 GMT — An samu rasa rayuka da dama yayin da jiragen yakin Isra’ila suka kai harin bam kan wani gida a Gaza

Wani harin jirgin yaki kan unguwar Zaytoun da ke birnin Gaza ya kashe akalla Falasdinawa takwas, kuma ya raunata da dama, a cewar wani jami’in kamfanin dillancin labarai na Falasdinu, WAFA.

Wakilin WAFA a yankin ya ce jiragen saman yakin Isra’ila sun kai hari ne kan wani gida a yankin, inda suka hallaka mutum takwas kuma suka raunata wasu da dama.

An garzaya da wadanda suka rasu da wadanda suka jikkata zuwa Asibitin al-Ahli Arab Hospital, wanda aka fi sani da al-Ma‘madani, da ke birnin, cewar rahoton na WAFA.

TRT Afrika da abokan hulda