Wani rahoton Hukumar kula da ƙwaya da aikata laifuka ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNODC, ya ce mutane miliyan 292 ne a faɗin duniya suka yi amfani da ƙwayoyi a 2022.
Hukumar ta ce shan ƙwaya ya ƙaru da kashi 20 cikin ɗari a shekaru 10 da suka gabata, inda ta ce ta yi imanin cewa cikin duk mutum 18 masu shekara 15 zuwa 64 a duniya, guda ya yi amfani da ƙwaya.
A 2022, "tabar wiwi" ita ce ƙwayar da aka fi amfani da ita, inda mutane miliyan 228 suka yi ta'ammali da ita; sai hodar ibilis, wadda mutum miliyan 60 suka yi amfani da ita. Akwai kuma amphetamines wadda mutum miliyan 30 suka yi amfani da ita, sai hodar ibilis, mutane miliyan 23.5, da kuma ecstasy mutane miliyan 20.
Rahoton kuma ya ce an samu gagarumar ƙaruwa a yawan mutanen da ke fama da cututtuka da suka danganci amfani da ƙwayoyi, inda ya ce mutane miliyan 64 sun samu matsalolin lafiya masu alaƙa da shan ƙwaya a 2022.
Rasa rayuka
Rahoton na UNODC ya ce ana rasa rayuwa sakamakon amfani da ƙwayoyi, inda ya yi nuni da cewa mutum miliyan 13.9 sun yi allurar ƙwaya a 2022, inda miliyan 1.6 suke da cutar HIV, sai miliyan 1.4 masu HIV da hepatitis C, sai kuma miliyan 6.8 masu hepatitis C kawai.
Haka kuma, UNODC ta bayyana cewa an sabu babbar ƙaruwa a samarwa da buƙatar hodar ibilis a duniya.
Kasuwar hodar ibilis a duniya tana ci gaba da ƙamari a ƙasashen Yamma da na Tsakiyar Turai da Amurka, amma tana yaɗuwa cikin sauri a ƙasashe masu tasowa da ke Afirka da Asiya, da kuma kudu maso gabashin Turai.
Sai dai rahoton ya yi nuni da cewa an samu gagarumar raguwa a haramtaccen noman opium a Afghanistan, wadda ita ce ƙasar da aka fi noma shi, inda aka samu raguwar kashi 95 a 2023 idan an kwatanta da 2022.
Raguwar da aka gani a Afghanistan ta faru ne saboda haramcin da Taliban ta yi kan noman opium a 2022, wanda ya tilasta wa manoma a ƙasar sauya abin da suke nomawa.