Hayaki na ci gaba da tashi a sararin samaniyar  Gaza a yayin da Isra'ila take kai hare-hare ta sama a yankin. An katse lantarki da kuma hana shigar da fetur Gaza. / Hoto: AA

1928 — Idan muka gama hare-harenmu a Gaza, to yankin zai sauya matuƙa: Mai bai wa Netanyahu shawara

Rundunar sojin Isra’ila na kai hare-hare ta ƙasa a Gaza kuma Gaza za ta yi matuƙar sauyawa, in ji Mark Regev, wani mai bai wa Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, a ranar Juma’a.

“Muna ƙara matsawa Hamas lamba. Muna ci gaba da matsa lambar da dama suke cikinta. Tuni mun fara kai hare-hare,” ya gaya wa kafar watsa labarai ta Fox News.

“Su za su ci gaba da shan wahala kuma sojojinmu za su ci gaba da kai hari har sai mun ragargaza makamansu tare da tarwatsa tsarin siyasarsu a Gaza. Idan muka kammala da wannan aikin, Gaza za ta yi matuƙar sauyawa,” ya ce.

1923 GMT — Mun shiryawa kutsen Isra'ila: Hamas

Hamas ta ce a shirye take da kutsen da Gaza take mata ta kasa, kamar yadda wani babban jami’in Hamas ya fada a ranar Juma’a bayan da Isra’ila ta sanar da cewa za ta fadada kai hare-hare ta kasa cikin yankin.

“Idan har Firaminista Benjamin Netanyahu ya yanke shawarar shiga Gaza a yau da daddare, to a shirye kungiyarmu take,” a sakon da babban jami’in Hamas na ofishin siyasa ya fada a shafin Telegram.

“Kasar Gaza za ta laƙume gawarwakin sojojinsa.”

1759 GMT — Rundunar sojin Isra’ila ta ce za ta ci gaba da “kai hare-hare ta kasa” a Gaza

Rundunar sojin Isra’ila ta ce za ta ci gaba da “kai hare-hare ta kasa” a Gaza a ranar Juma’a da daddare bayan da ta zafafa kai hare-haren sama a yankin na Falasdinu.

“Bayan jerin hare-haren da aka kai a kwanakin da suka gabata, dakarun sojin kasa suna fadada kai hare-hare ta kasa a yau da daddare,” a cewar mai magana da yawun rundunar sojin Daniel Hagari, kamar yadda ya shaida wa manema labarai.

Sanarwar tasa ta biyo bayan shafe darare biyu da aka yi ana kai hare-hare da tankokin yaki cikin Gaza.

1258 GMT — Falasɗinawa sun yi zanga-zanga a gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye don goyon bayan Gaza

Daruruwan Falasdinawa ne suka yi zanga-zanga a kan titunan birnin Ramallah a Gabar Yammacin Kogin Jordan, inda da yawan su suka bayyana goyon bayansu ga Hamas a yayin da Isra'ila ke tsaka da yaƙinta a kan Gaza.

Mutanen sun yi ta sowar ambaton kalaman "a sakar wa Gaza mara" da kuma "mutane na son rundunar Al Qassam" wato wani reshen ƙugniyar Hamas. Sauran kuwa na ɗaga tutoci ne da ƙyallayen da ke nuna goyon bayan fafutukar Falasɗinawa.

Fakhi Barghouti mai shekara 80, ya ce Falasɗinawa a Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye "na buƙatar ƙara zage dantse a kan yaƙin Gaza."

1217 GMT — Falasdinawan da suka mutu a hare-haren Isra'ila a Gaza sun kai 7,300

Yawan Falasɗinawan da suka mutu a sakamakon hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza sun kai 7,326, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Gazan.

Ashraf al Qidra, wani mai magana da yawun ma'aikatar, a wajen wani taron manema labarai ya ce: "Yawan waɗanda suka mutu a Gaza sakamakon kutsen da Isra'ila ke yi ya kai 7,326, ciki har da yara 3,038, da mata 1,726 da kuma tsofaffi 414. Sannan ƴan ƙasar 18,484 ne suka ji raunuka tun daga ranar 7 ga watan Oktoban.

Ya fayyace cewa "A sakamakon mamayar da Isra'ila ke yi ta aikata kishan kiyashi sau 41 a cikin awannin da suka wuce, inda mutum 298 suka yi shahada, wadanda da yawansu aka raba su da muhallansu suka koma kudancin Gaza.

Ya kuma zarfi Isra'ila "da aikata kisan kiyashi sau 772 da gangan a kan iyalai da dama."

"Mun samu rahotannin ɓatan mutum 1,700 da suka haɗa da yara 940 da har yanzu suke ƙarƙashin baraguzai," a cewar mai magana da yawun ma'aikatar.

1030 GMT — "Mutane da dama za su sake mutuwa" a Gaza, in ji MDD

Muhimman kayan da ake bukata na karewa, magunguna sun kusa ƙarewa da abinci da ruwan sha ma na ƙarewa, Zirin Gaza na rushewa.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan cewa ‘wasu da yawa za su mutu’ sakamakon ci gaba da yi wa Zirin Gaza ƙawanya da Isra’ila ke yi.

“A yayin da muke magana a yanzu mutane na mutuwa a Zirin Gaza, ba wai bama-bamai kadai ne ke kashe su ba, wasu za su ci gaba da mutuwa saboda tasirin ƙawanyar da aka yi wa Zirin Gaza,” in ji Philippe Lazzarini, babban kwamishinan MDD kan hukumar da ke kula da Falasdinawa ‘yan gudun hijira.

“Muhimman kayan da ake bukata na karewa, magunguna sun kusa ƙarewa da abinci da ruwan sha ma na ƙarewa, Zirin Gaza na rushewa.”

0951 GMT — MDD na damuwa ‘ana aikata laifukan yaki a rikicin Zirin Gaza’

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana duba yiwuwar bayyana cewa ana aikata laifukan yaki a rikicin da ake yi tsakanin Isra’ila da Hamas.

“Mun damu kan yadda ake aikata laifukan yaki. Mun damu matuka kan mawuyacin halin da ake jefa jama’ar Zirin Gaza sakamakon harin da Hamas ta kai, wanda shi ma laifin yaki ne,” in ji kakakin Ofishin Kare Hakkokin Dan Adam Ravina Shamdasani yayin gana wa da manema labarai a Geneva.

5:00 GMT - Harin makami mai linzami ya fada garin Taba da ke gabar Tekun Maliya a Masar

Wani harin makami mai linzami ya fada kan wata cibiyar lafiya a wani gari da ke gabar Tekun Maliya a kan iyakar Masar da Isra'ila, inda ya yi sanadin ji wa mutum shida rauni, kamar yadda kafar watsa labarai ta Masar Al Qahera , ta rawaito.

Da take ambatar majiyoyi, Al Qahera ta rawaito cewa harin na garin Taba ya shafi yaƙin da ake yi da ƙungiyar Hamas ta Falasdinu da kuma Isra'ila ne.

Wani ganau a Taba, garin da ke da nisan kilomita 220 daga Zirin Gaza, ya ce ya ji ƙarar fashewa tare da hango hayaƙi da ƙura suna tashi.

TRT Afrika da abokan hulda