MDD ta ce yara 10 a rana suna rasa kafa daya ko biyu sannan Falasdinawa rabin miliyan na fama da matsananciyar yunwa / Photo: Reuters

1414 GMT — Yara 10 suna rasa ƙafa ɗaya ko biyu a duk rana a Gaza - MDD

Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sun yi kakkausar suka game da rikicin Gaza da yaki ya daidaita, suna masu cewa yara 10 a rana suna rasa kafa daya ko biyu sannan Falasdinawa rabin miliyan na fama da matsananciyar yunwa.

Isra'ila na ci gaba da ta'azzara hare-haren da take kai wa Gaza da kuma hare-hare kan kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas sakamakon harin na ranar 7 ga watan Oktoba, yayin da ta ci gaba da killace yankin na mutane miliyan 2.4.

Jami'an Falasdinawa sun ce wani harin ya kashe mutum 10 'yan gidan shugaban siyasar Hamas Ismail Haniyeh ciki har da 'yar'uwarsa.

Sojojin Isra'ila ba su tabbatar da kai harin ba, wanda hukumar kare fararen hula a Gaza ta ce an kai harin ne a gidan 'yan'uwan shugaban da ke arewacin sansanin 'yan gudun hijira na Al Shati, inda ɓaraguzan gini ya danne wasu gawarwakin.

1043 GMT –– Ana ci gaba da fuskantar tsananin yunwa a dukkan yankunan Gaza — global hunger monitor

Ana ci gaba da fuskantar yiwuwar faɗawa cikin bala'in yunwa a dukkan yankunan Gaza a yayin da Isra'ila take ci gaba da kai hare-hare a yankin sannan ta taƙaita agajin da ake shigarwa, a cewar ƙungiyar global hunger monitor.

Fiye da mutum 495,000, wato sama da kashi ɗaya cikin biyar na al'ummar yankin Gaza na fuskantar masifar yunwa da rashin abinci, in ji ƙungiyar.

Ta ƙara da cewa da alama abincin da aka kai arewacin Gaza a watan Maris da Afrilu ya rage fuskantar yunwa a wasu yankuna.

0447 GMT –– Isra'ila ta kai harin bama-bamai a Gaza yayin da Amurka ta yi gargaɗi kan yaƙi a Lebanon

Isra'ila ta ci gaba da yin luguden wuta a Gaza bayan Firaminista Benjamin Netanyahu ya ce ana kawo ƙarshen matakin "yaƙi mai tsanani", a yayin da Amurka ta yi kira ga ƙawarta ta guji faɗaɗa yaƙi a kan iyakar Lebanon.

Dakarun Isra'ila sun tsananta kai hare-hare, inda suka kashe mutum 13 a wasu makarantu biyu da kuma wani gida a Gaza, a cewar rundunar 'yan bijilanti da ke ƙarƙashin ƙungiyar Hamas.

A yayin da Isra'ila take shirin tura sojoji daga Gaza zuwa kan iyaka da Lebanon, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken a ranar Litinin ya gargaɗi ministan tsaron ƙasar da kada ya bari wannan yaƙin ya yi ƙamari.

Isra'ila tana ci gaba da yin luguden wuta a Gaza / Hoto: AA

2133 GMT —Blinken ya faɗa wa Gallant na Isra'ila a rage zaman tankiya da Hezbollah

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken ya roƙi Ministan Tsaron Isra'ila da ke ziyara Yoav Gallant ya kauce wa ci gaba da yaƙi da Hezbollah ta Lebanon, a yayin da yaƙin ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza da aka mamaye ke ci gaba, kamar yadda kakakin Ma'aikatar ta Harkokin Waje ya bayyana bayan taronsu.

Blinken ya kuma jaddada buƙatar ɗaukar matakai na tabbatar da kare ma'aikatan agaji a yankin da aka mamaye.

Blinken "ya jaddada muhimmancin kauce wa ƙaruwar yaƙi da kuma cim ma mafita ta diflomasiyya wacce za ta bai wa iyalai 'yan Isra'ila da 'yan Lebanon damar komawa gidajensu," a cewar mai magana da yawun Ma'aikatar ta Harkokin Waje Matthew Miller.

Sanarwar ta Miller na zuwa ne a daidai lokacin da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi barazanar mamayar sojoji a Lebanon.

'Yan kwanaki kaɗan da suka wuce ne, sojojin Isra'ila suka ce "sun amince sun kuma yi nazari" kan shirin mamaye Lebanon, duk da cewa Amurka na yin aiki don hana rikiɗewar kai hare-hare da aka shafe watanni ana yi kan iyakar ƙasashen zuwa cikakken yaƙi.

Wata wuta da ta tashi a ɓangaren Isra'ila kan iyakarta da Lebanan a lokacin da ake musayar wuta tsakanin Hezbullah da sojojin Isra'ila / Hoto: Reuters

2022 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 5, 4 daga cikinsu yara ne a Gaza

Isra'ila ta kashe mutum biyar, ciki har da yara huɗu, sannan ta jikkata aƙalla mutum goma bayan kai wani hari a tsakiyar Gaza, a cewar jami'an asibiti.

An kai waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata daga sansanin Maghazi zuwa Asibitin Shahidai na Al Aqsa a yankin Deir al-Balah dake kusa, inda wani ɗan jaridar Associate Press ya gan su.

Wata yarinya da fuskarta ta ɓaci da jini da ƙura, ta ringa karkarwa lokacin da aka yi gaggawar fita da ita daga motar ɗaukar marasa lafiya aka ɗora ta a kan gado.

Sauran mutanen da suka jikkata sun kwanta ko kuma sun zauna a daɓen asibiti, yayin da mutane suke riƙe da ledar ƙarin ruwa a hannayensu.

A cikin yanayi na damuwa, an kai waɗanda suka mutu ɗakin ajiye gawawwaki na asibitin. Hukumomi sun ce shekarun yaran sun kama daga 4, da 9, da 13, da 16.

TRT Afrika da abokan hulda