Yahudawa 'yan kama wuri zauna sun dirar wa harabar Masallacin Ƙudus. / Photo: AA

1012 GMT — Yahudawa 'yan kama wuri zauna sun dirar wa harabar Masallacin Ƙudus

Gomman Yahudawa 'yan kama wuri zauna sun shiga harabar Masallacin Ƙudus da ke gabashin Birnin Kudus da ke karkashin kariyar tsaron Isra'ila, ta ƙarfin tsiya.

Kamfanin dillancin labaran Falasdinu na Wafa ya rawaito wasu shaidu a cikin masallacin wadanda suka ce Yahudawa da dama ne suka kutsa kai cikin masallacin, tare da yin zagayen da ya tunzura jama'a a ciki, suka kuma gudanar da ayyukan ibada na Talmud.

Dakarun Isra'ila sun tsaurara matakan tsaro na hana masu ibada shiga masallacin, yayin da aka jibge ɗaruruwan sojojin Isra'ila a yankin tsohon Birnin Ƙudus da zai sada ka da Masallacin Ƙudus ɗin, kamar yadda Wafa ya ƙara da cewa.

0750 GMT — Isra'ila ta yi luguden wuta a sassa da dama na Gaza a yayin da yaƙi ya yi ƙamari a Rafah

Dakarun Isra'ila sun yi luguden wuta a sassa da dama a faɗin yankin Gaza, sannan mazauna Rafah sun bayar da rahoton yin gumurzu a yankin na kudancin Falasɗinu.

Ganau sun ce yaƙi ya yi ƙamari a yankin Tel Al Sultan na yammacin Rafah, inda tankokin yaƙi suka riƙa ƙoƙarin kutsawa arewaci ana tsaka da ba-ta-kashi. Mayaƙan Hamas da Islamic Jihad sun ce sun yi amfani da rokoki da bama-bamai wajen kai hari kan dakarun Isra'ila.

Tun a watan Mayu, Isra'ila ta mayar da hankali wurin kai hari ta ƙasa a Rafah, da ke kan iyakar Gaza da Masar, inda kusan rabin mutane miliyan 2.3 na Gaza suke samun mafaka bayan sun tsere daga arewaci. Tuni dai mutane suka riƙa tserewa daga yankin.

Ma'aikatan lafiya sun ce Isra'ila ta kashe Falasɗinawa biyu a harin da ta kai da makami mai linzami a Rafah ranar Laraba da safe..

2123 GMT — 'Yan Houthi sun yi iƙirarin 'kai hari' kan jirgin ruwan Isra'ila a Tekun Arabiya

Mayaƙan Houti sun ce sun yi amfani da wani sabon makami mai linzami wajen kai hari kan jirgin ruwan MSC Sarah V a Tekun Arabiya, inda suka ɗauki nauyin kai harin da aka bayar da rahotonsa.

Yahya Sarea, mai magana da yawun ƙungiyar, ya yi iƙirarin cewa harin "ya afka kuma ba kuskure" kan jirgin ruwan, yana bayyana jirgin da cewa "na Isra'ila" ne.

Cibiyar The United Kingdom Maritime Trade Operations ta ce an ba da rahoton cewa ma'aikatan jirgin suna cikin ƙoshin lafiya, sannan jirgin ya nufi tashar da zai tsaya ta gaba.

'Yan Houthi suna kai hari kan abin da suka ce jiragen Isra'ila ne ko kuma za su je Isra'ila a Kogin Maliya da wasu wuraren a matsayin martani kan yaƙin kisan kiyashi a Gaza. / Hoto: Reuters Archive

2225 GMT — Sojojin Amurka sun gayyaci 'yan jarida zuwa shirin kai agaji Gaza ta ruwa

Bayan jeka ka dawo da dama, shirin nan na kai agaji Gaza na $230 miliyan ya dawo ka'in da na'in.

Rundunar sojan Amurka ta gayyaci 'yan jarida zuwa wata ziyara, wacce ta zama karon farko da 'kafofin watsa labari na duniya suka shaida yadda ake aikin agajin.

Yayin da 'yan jarida ke duba abin da ke faruwa, su kuma sojojin Amurka riƙe da bindigogi ƙirar mashinga suna jagorantar aikin. Jiragen Amurka maƙale da kayan agaji sun tsaye a wajen.

Isra'ila ta hana 'yan jaridar ƙasashen waje kawo rahotannin yaƙin da ake yi a Gaza, mafi yawan labaran 'yan jarida Falasɗinawa na cikin gida ne suke bayar da su. Isra'ila ta kashe fiye da 'yan jarida 150, ta kuma jikkata wasu gommai tun daga watan Oktaban bara.

TRT World