Hare-haren sama na Isra'ila sun kashe mutane 19 a Lebanon cikin sa'o'i 24 da suka gabata / Hoto: AA / Photo: AFP

Alhamis, 24 ga watan Oktoba, 2024

1524 GMT — Akalla mutane 19 ne aka kashe a hare-haren Isra’ila a Lebanon cikin sa’o’i 24 da suka gabata, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu ya kai 2,593, a cewar gwamnatin Lebanon.

2341 GMT — Isra'ila ta yi luguden wuta a kudancin Beirut

Jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hari ta sama fiye da 17 a yankunan da ke wajen kudancin Beirut babban birnin Lebanon, a wani matai da ake gani a matsayin ɗaya daga cikin manyan hare-hare da ta ka a birnin.

Kamfanin dillancin labarai na Lebanon, National News Agency (NNA), ya ruwaito cewa Isra'ila ta kai hare-hare huɗu ta sama a yankin Laylaki, waɗanda suka rusa rukunin gidaje shida tare da haddasa gobara da ta watsu zuwa sauran sassan yankin.

Ya ƙara da cewa jirin yaƙin Isra'ila ya rusa ofishin gidan talbijin na Al Mayadeen TV wanda ake alaƙantawa da ƙungiyar Hezbollah, wanda ke cikin rukunin wasu gine-gine.

Ƙarin labarai 👇

0151 GMT — Isra'ila ta kai hari kan wasu gidajen jama'a a Damascus

Kafar watsa labarai t gwamnatin Syria ta ce Isra'ila ta kai hari a wani gini da jama'a ke zama a birnn Damascus.

"Rahotannin da aka fara samu sun nuna cewa Isra'ila ta kai hari a wani gini da jama'a ke zama a yankin Kafr Sousa na birnin Damascus," a cewar kamfanin dillancin labarai na Sana, ko da yake bai yi ƙarin bayani ba.

2206 GMT — Rundunar Gaza Civil Defense ta daina aiki a arewacin yankin

Rundunar bayar da agajin gaggawa ta Gaza ta sanar da dakatar da aiki a arewacin yankin sakamakon kamun da dakarun Isra'ila suka yi wa jami'anta guda biyar da kuma kai wa uku hari.

Kazalika rundunar ta ce an lalata injinta na wutar lantarki ɗaya tilo da ke yankin, inda ta bayyana matakin a matsayin "babban bala'i."

"Mun daina aiki gaba ɗaya a Arewacin Gaza, kuma yanayin da ake ciki ya zama wani babban bala'i. Yanzu mazauna yankin ba su da kayan buƙatun gaggawa," in ji wata sanara da rundunar ta fitar.

TRT World