Hamas ta yi gargadi kan tsokanar da Isra'ila ke yi a Masallacin Ƙudus / Photo: Reuters Archive

Juma'a, 13 ga watan Satumban 2024

1337 GMT — Hamas ta yi gargadi kan tsokanar da Isra'ila ke yi a Masallacin Ƙudus

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi wani kakkausan gargadi, inda ta yi Allah wadai da tsokanar da Isra'ila ke yi a Masallacin Ƙudus a baya-bayan nan, tare da ayyana hakan a matsayin wani abu mai hatsarin gaske.

A baya-bayan nan wata kungiyar masu tsattsauran ra'ayin Isra'ila mai suna Temple Mount Faithful, ta fitar da wani bidiyo da ke nuna yadda wata gobara ta kama da ta cinye Masallacin Ƙudus da Dome of the Rock, tare da taken, "Zuwa nan ba da jimawa ba a cikin wadannan kwanaki."

Kungiyar da ta shahara da kiran rusa Al-Aqsa tare da maye gurbinsa da wajen ibada na Yahudawa, ta haifar da fushi saboda sakin bidiyon.

Kungiyar Hamas ta yi Allah-wadai da wannan bidiyo a zaman wani yunkuri na tunzura jama'a da kungiyoyin masu tasurin ra'ayi na Isra'ila ke ci gaba da yi, wadanda ta ce suna gudanar da ayyukansu a karkashin kariyar gwamnatin Isra'ila.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta yi gargadin cewa wadannan ayyuka na da nufin "Mayar da masallacin na Yahudawa da kuma goge matsayinsa na Musulunci."

1612 GMT — Harin jiragen yakin Isra'ila ya kashe mutum 1 tare da raunata 4 a kudancin Lebanon

Wani jirgin yakin Isra'ila ya kashe mutum daya tare da jikkata wasu hudu a wani hari da ya kai a garin al-Ahmadiya da ke kudancin kasar Lebanon, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar Labanon ya bayyana.

Kamfanin ya bayyana cewa harin da jirgin mara matuki ya kai kan wani gida a garin, ya yi sanadin jikkatar mutane da dama.

Daga baya, ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta tabbatar da adadin farko: mutum daya ya mutu, wasu hudu kuma sun jikkata, ciki har da wani yaro. Ma'aikatar ba ta bayyana munin raunin da aka samu ba.

1503 GMT Hamas ta yaba wa Chile da shiga shari'ar kisan kiyashi da Afirka ta Kudu ke yi wa Isra'ila

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi marhabin da sanarwar da Chile ta bayar ta shiga cikin shari'ar kisan kiyashin da ake yi wa Isra'ila wadda Afirka ta Kudu ta shigar a kotun kasa da kasa (ICJ) kan yakin da take yi da Gaza.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta ce sanarwar ta Chile ta nuna matsayinta ga bil'adama, daukar dabi'un dan'adam, da kuma watsi da keta dokokin kasa da kasa.

Kungiyar Falasdinu ta kuma yaba wa shugaban kasar Chile, Gabriel Boric saboda "taimaka wa 'yancin al'ummar Falasdinu da gwagwarmayar neman 'yanci da cin gashin kansu."

Hamas ta bukaci kasashen duniya da su shiga shari'ar kisan kare dangi da ake yi wa Isra'ila a gaban kotun ICJ da kuma kara matsa lamba kan Isra'ila kan ta dakatar da yakin da take yi a Gaza.

TRT World