Israeli soldiers operate in the Gaza Strip / Photo: Reuters

1331 GMT — Hamas ta fafata da dakarun Isra’ila a kan take dokokin yarjejeniyar tsagaita wuta

Rundunar Qassam Brigades ta ƙungiyar Hamas ta fafata da dakarun Isra’ila a kan take haƙƙoƙin yarjejeniyar tsagaita wuta a arewacin Gaza.

Kungiyar ta yi kira ga masu shiga tsakani da su tabbatar da aiwatar da cika sharuddan tsagaita wuta a Isra'ila.

Hotunan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta kan yarjejeniyar farko ta kwanaki hudu sun nuna Falasdinawa na tserewa daga harbe-harbe yayin da sojojin Isra'ila suka hana mazauna yankin komawa arewacin Gaza a lokacin da aka tsagaita wuta na wucin gadi.

Kafin a fara tsagaita wuta sojojin Isra'ila sun jefar da takardu suna gargadin mutane da ka da su yi yunkurin komawa yankin.

1355 GMT — Shugaban CIA, Mossad da Firaiministan Qatar za su tattauna

Daraktan Hukumar Leken Asiri ta CIA Bill Burns zai tattauna da daraktan Hukumar Leken Asiri ta Mossad David Barnea da Firaiministan Qatar Mohammed Bin Abdul Rahman al Thani a Doha a ranar Talata.

Taron zai fi mayar da hankali wurin tattaunawa kan yiwuwar tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta, domin kara musayar karin fursunoni, kamar yadda kafar watsa labarai ta Axios ta bayyana, inda ta ruwaito wani jami’in Amurka da wasu majiyoyi biyu masu karfi.

1300 GMT Mutane na cikin hatsarin mutuwa daga cututtuka fiye da bama-bamai a Gaza: WHO

Akwai fargabar karin mutane za su iya mutuwa sakamakon cututtuka fiye da hare-haren da Isra’ila ke kaiwa a Gaza idan ba a kai agaji bangaren lafiya na kasar ba, kamar yadda mai magana da yawun Hukumar Lafiya ta Duniya ta tabbatar.

“A hankali za mu ga karin mutane suna mutuwa daga cututtuka fiye da hare-hare idan ba mu gyara tsarin lafiya ba,” kamar yadda Margaret Harris ta bayyana, mai magana da yawun WHO.

Ta bayyana cewa rufewar asibitin Al Shifa da ke arewacin Gaza a matsayin “bala’i” inda ta bayyana damuwarta kan ci gaba da tsare wasu daga cikin jami’anta da dakarun Isra’ila suke yi.

0800 GMT — Adadin mutanen da Isra'ila ta kashe Gabar Yamma da Kogin Jordan

Harbin da sojojin Isra'ila suka yi ya kashe Bafalasdine na biyu a kusa da birnin Ramallah a Gabar Yammacin Kogin Jordan.

Majiyoyi daga Asibitin Gwamnati na Salfit sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa, "An kawo wani mutum daga garin Kafr Ayn na arewa maso yammacin Ramallah sashen kula da marasa lafiya na gaggawa dauke da ciwuka na harbin bindiga mai muni, kuma ya mutu."

Hukumomi a garin na Kafr Ayn sun ce "wasu sojojin Isra'ila sun je garin inda suka kama mutumin, abin da ya kai ga arangama tsakaninsu da gomman Falasdinawa."

Ganau sun bayyana cewa "sojojin sun harba harsasai kan mutane abin da ya jikkata Malik Al Barghouthi bayan harsasai uku sun same shi. Daga nan ne aka kai shi Asibitin Gwamnati na Salfit, inda aka sanar da rasuwarsa.

A wani labarin kuma, dakarun Isra'ila sun kashe wani Bafalasdine ranar Litinin da maraice a Yammacin birnin Ramallah da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye.

Adadin mutanen da Isra'ila ta kashe Gabar Yamma da Kogin Jordan ya karu zuwa 242 tun ranar 7 ga watan Oktoba, a cewar ma'aikatar lafiya.

0639 GMT Har yanzu akwai kusan Falasdinawa '60 da ke gidan yarin Isra'ila'

Wata kungiya mai zaman kanta ta bayyana cewa har yanzu akwai matan Falasdinawa 60 da ke gidan yarin Isra’ila tun bayan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.

Amal Sarahneh wadda jami’ar watsa labarau ce a kungiyar Palestinian Prisoners Society ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa Isra’ila ta kama matan Falasdinawa 56 da mata a kame-kamen da suke yi a Gabar Yamma da Kogin Jordan da Gabashin Birnin Kudustun bayan 7 ga watan Oktoba inda suka kama mutum 3,260.

Sarahneh ta kara da cewa Isra’ila ta saki Falasdinawa mata 33 karkashin yarjejeniyar musayar fursunoni da kungiyar Hamas a kwanaki hudu da suka gabata.

0400 GMT — Kwararru na Majalisar Dinkin Duniya sun nemi a yi bincike mai zaman kansa kan laifukan da aka aikata a Isra'ila da Falasdinu

Wasu kwararru na Majalisar Dinkin Duniya sun yi kira a gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa kan laifukan da aka aikata a Isra'ila da Falasdinu a wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar ranar Litinin.

Da suke kira ga Isra'ila da hukumar Falasdinawa a Gabar Yammacin Kogin Jordan da hukumomin Gaza da su ba da cikakken hadin kai don yin binciken, sun ce "dole ne a bai wa masu bincike masu zaman kansu abubuwan da suka dace da goyon baya da samun damar da ake bukata don gudanar da bincike cikin gaggawa, da kuma nuna rashin son kai kan laifukan da ake zargin aikatawa a dukkan bangarorin da ke rikici.

"Aikin binciken laifuffukan yaki da cin zarafin bil adama, da suka hada da duk wani aiki na takaitawa ko kisan gilla da azabtarwa ko wasu cin zarafi kan mutuncin dan'adam, wani muhimmin al'amari ne na shari'a," in ji su.

Sun kuma yi kira ga kasashen duniya da su yi aiki domin ganin an gaggauta hukunta duk wadanda ke da hannu wajen aikata laifukan yaƙi da cin zarafin Bil'adama da kuma sauran laifukan da suka shafi kasa da kasa a rikicin, musamman wadanda ke da alhakin gudanar da ayyukansu.

0330 GMT — Shugaban Hamas a Gaza ya gana da wasu Isra'ilawa da aka yi garkuwa da su: Kafofin yada labaran Isra'ila

Shugaban kungiyar Hamas ta Falasdinawa a Gaza, Yahya Sinwar, ya gana da wasu mutanen Isra'ila da aka yi garkuwa da su a cikin ramukan ƙarƙashin ƙasa a Zirin Gaza, kamar yadda kafafen yada labaran Isra'ila suka rawaito.

Akalla daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su ya ce Sinwar ya yi magana da su cikin harshen Larabci, kamar yadda jaridar Haaretz ta ruwaito.

Ya ce musu suna cikin aminci tare da Hamas kuma kada su ji tsoro. Tashar talabijin ta Channel 12 ta Isra'ila ta bayar da rahoton cewa hukumar tsaron Isra'ila ta tabbatar da labarin.

2317 GMT — Isra'ila ta saki kananan yara Falasdinawa 30 da mata uku a yarjejeniyar musaya da Hamas

Isra'ila ta saki ƙananan yara Falasdinawa 30 da mata uku "a cikin dare" karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta da ta mayar da fursunonin yankin Gaza da aka yi wa ƙawanya.

Sakin dai ya kawo adadin mata da yara ƙanana Falasdinawa da Isra'ila ta sako a cikin kwanaki hudu na farko na dakatar da yaƙin zuwa 150.

Wadanda aka sako da sanyin safiyar Talata sun hada da Bafalasdiniya mafi ƙarancin shekaru a cikin mutanen, Nofuz Hammad, ‘yar shekara 16, daga unguwar Sheikh Jarrah da ke gabashin Birnin Ƙudus da aka mamaye, wacce hukumomin Isra’ila suka daure ta shekaru 12 a gidan yari, kuma a yanzu suka sake ta a yarjejeniyar musanya ta Hamas da Isra’ila, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Anadolu ya ruwaito.

Bafalasdine Muhammad Abu Al-Humus, tsohon fursuna daga gidan yarin Isra'ila wanda aka sako a yanzu, ya samu tarba daga iyalansa da danginsa bayan ya koma gidansa da ke gabashin Birnin Kudus, a ranar 28 ga Nuwamba, 2023.. / Photo: AFP

2313 GMT — Netanyahu ya amince da sanya Falasdinawa mata 50 cikin jerin sunayen waɗanda za a saka

Ofishin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce ya amince da saka wasu Falasdinawa mata 50 a cikin jerin sunayen da za a sake su idan har an sako wasu 'yan Isra'ila da aka yi garkuwa da su daga Gaza.

Sanarwar ta zo ne bayan da masu shiga tsakani na Qatar suka ce tsagaita wuta ta kwana hudu ta amince da ba da damar musayar fursunonin da Isra'ila ke tsare da su, da Falasdinawan da ke cikin gidajen yarin na Isra'ila wanda ya kamata ya ƙare bayan da aka tsawaita wa'adin kwanaki biyu a ranar Litinin.

TRT Afrika da abokan hulda