Bakin masanan ya zo daya kan cewa ko dai Gaza za ta jawo Majalisar Dinkin Duniya ta “sake farfadowa ko kuma za ta zo karshe Photo: TRT World

A wani daki mai cike da mutane a rana ta farko na taron diflomasiyya na Antalya Diplomacy Forum, wato wani taro na tattaunawa tsakanin masu tsara manufofin kasashe da tsofaffin ma’aikatan diflomasiyya da masu bayar da shawarwari ga gwamnati a matsayin wani mataki na kawo karshen yake-yake ciki har da na Isra’ila da Falasdinawa.

Bakin masanan ya zo daya kan cewa ko dai Gaza za ta jawo Majalisar Dinkin Duniya ta “sake farfadowa ko kuma za ta zo karshe”, inda mutane da dama suke ganin wannan ci gaba da yakin da Isra’ila take yi zai ci gaba da gwara kan manyan kasashen duniya.

Yayin da yake bayani kan yadda yakin da ake yi Gaza zai yi tasiri kan makomar Majalisar Dinkin Duniya, wani tsohon jami’in diflomasiyya Masar da yake halartar taron Hesham Youssef wanda yanzu babban jami’I ne a Cibiyar Zaman Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ya shaida wa TRT cewa “akwai wani abu mai kayatarwa da yake faruwa da Amurka a yanzu”.

“Kamar yadda ka sani, [galibi] al’amuran harkokin kasashen waje ba sa tasiri a Majalisar Dinkin Duniya. [Amma] akwai rahoton na baya-bayan nan da ke cewa halin da ake ciki a Gaza za su iya yin tasirin a kan Babban Zaben Amurka da ke take,” in ji shi Youssef.

“Kasar Amurka ta shiga yaki da Afghanistan da yaki da kuma Iraqi, amma kuma hakan ba zai yi tasiri a kan sakamakon zaben ba, sai dai wannan yakin da ake yi a Gaza zai iya yin tasiri kan zaben Amurka.”

Yayin da ake yin zanga-zangar kin jinin yaki da karuwar nuna goyon baya ga Falasdinawa a tsakanin mazauna Amurka, Shugaban Amurka Joe Biden yana fuskantar babban kalubale daga bangaren “’yan jam’iyyar Democrat da ke masa bore” dangane da yakin Gaza.

Rahotanni masu zaman kansu da dama na nuni da cewa yaƙin neman zaɓensa ya gaza farawa da zarafi da kuma sha'awa - a wani ɓangare na sukar da ake yi tsakanin 'yan Jam'iyyar Democrat da ke nuna rashin jin daɗinsa kan matakin da ya dauka kan hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza.

Masu fafutuka a Michigan - jihar da a al'adance ta dogara ga Democrat a zabukan shugaban kasa - sun nemi mutane da su shiga zaben zanga-zangar ta hanyar janye goyon bayansu ga Biden yayin zaben fitar da gwani na Democrat.

Suna fatan samun ƙuri'u 10,000 "da ba na kowa ba", amma masu jefa kuri'a 100,000 sun gama amsa kiran nasu - babbar alama ce cewa goyon bayan Biden ga Isra'ila na iya sawa ya rasa jihar.

Ana fatan taron diflomasiyya na Antalya zai kawo sauyi a yadda ake gudanar da al'amuran duniya.

Turkiyya na da kyakkyawan matsayi don neman dawo da MDD da kuma amintaccen tsari ga Gaza da Yammacin Kogin Jordan - kamar yadda aka yi a Gabashin Timor - kuma a matsayin mamba ta NATO, don ba da shawarar cikin gida don amfani da ita wajen tabbatar da tsaro a cikin yankin mai tsarki," in ji Swisher yayin da ake muhawara kan bukatar masu shiga tsakani na gaggawa a rikicin Isra'ila da Falasdinu.

Dangane da rashin amincewar Amurka na daukar tsauraran matakai kan Isra'ila, Swisher ya ce har yanzu MDD tana da damar da za ta ci gaba da kasancewa tare da hadin gwiwa idan gamayyar ƙawance ya matsa lamba kan Washington tare da matsa ƙaimi wajen kawo sauyi da manufofin da za su bude wa wasu bangarori damar jagorantar yunƙurin diflomasiyya don fara tattaunawa mai ma'ana tsakanin Isra'ila da Falasdinu.

“Gaskiyar magana ita ce Amurka ta tabbatar ba za ta iya tafiya ita kadai ba; ta shiga siyasar cikin gida ta Isra'ila dumu-dumu wajen goyon bayanta da take yi - musamman a yanzu a cikin shekarar zabe," in ji shi.

Ya ce dole ne jami'an diflomasiyya su binciki zaɓin tabbacin tsaro wanda "zai iya gamsar da kowane bangare kaɗan, ciki har da tura dakarun wanzar da zaman lafiya na Amurka, mai yuwuwa rundunar NATO ta ƙarfafa gwiwa."

TRT World