Fiye da mutum miliyan 345 na fuskantar matsanancin karancin abinci a wannan shekarar./Hoto:Reuters

Matsalar yunwa da ke addabar duniya ta sa fiye da mutum miliyan 700 ba su da tabbacin yadda za su samu abinci a kullum, yayin da bukatar abincin ke karuwa a daidai lokacin da matsalar rashin jinkai ke ta’azzara, a cewar shugabar Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya.

Cindy McCain ta shaida wa Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ranar Alhamis cewa rashin isassun kudi ya sa hukumarta ta rage tallafin abincin da take bai wa miliyoyin mutane, kuma za ta “ci gaba da ragewa”.

“Muna fama da rikice-rikice iri-iri masu tasiri a yanzu da wadanda za su yi tasiri nan gaba da za su ta’azzara matsalar jinkai a duniya,” in ji ta. “Wannan shi ne ainihin abin da ke faruwa — a fili karara — kuma za mu yi fama da tasirin wadannan rikice-rikice nan da shekaru masu zuwa.”

Shugabar Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniyar ta kiyasta cewa kusan mutum miliyan 47 a kasashe fiye da 50 na dab da fadawa cikin tsananin yunwa — kana yara miliyan 45 ‘yan kasa da shekara biyar na fama da tamowa.

A cewar Hukumar, a kasashe 79 da take gudanar da ayyukanta kimanin mutum miliyan 783 — daya bisa 10 na yawan mutanen duniya — suna kwanciyar barci kullum ba tare da sun sanya komai a bakinsu ba.

Fiye da mutum miliyan 345 na fuskantar matsanancin karancin abinci a wannan shekarar, wato an samu karin mutum miliyan kusan 200 kenan daga farkon 2021 kafin annobar Covid-19, in ji hukumar.

Hukumar ta ce rikice-rikice da tabarbarewar tattalin arziki da sauyin yanayi da tashin farashin takin zamani ne suka ta’azzara matsalar.

AP