1018 GMT — Akalla mata 180 ke haihuwa a kullum a Gaza duk da takunkuman lafiya da Isra’ila ta saka
Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta ce akalla mata 180 ne ke haihuwa a kowace rana a Gaza a karkashin yanayi mai hadari da rashin mutuntaka sakamakon hare-haren da Isra'ila ke kaiwa.
“A Gaza, mata 180 ne ke haihuwa a kullum a cikin yanayi mai hadari da rashin jin dadi. Da yawa daga cikinsu ba sa iya isa asibitoci saboda kasancewarsu a yankunan da aka yi wa kawanya, inda sojojin Isra'ila suka hana motocin daukar marasa lafiya isa zuwa gare su,” kamar yadda ta bayyana a sanarwar.
0940 GMT — Falasdinawa 800,000 a Gaza na fuskantar 'barazanar mutuwa saboda yunwa'
Ofishin wata labarai na Gaza ya bayyana cewa mazauna birnin da kewaye 800,000 na fuskantar barazanar mutuwa sakamakon tsarin Isra’ila na horas da su da yunwa da kishirwa.
A wata sanarwa da ofishin ya fitar, ya bayyana cewa Gaza da arewacinta na bukatar motocin abinci 1,300 a ullum domin magance matsalar yunwa.
Ta bayyana cewa arewacin Gaza kadai na bukatar manyan motoci 600 na abinci sai kuma birnin na Gaza motoci 700.