Fadan da ake gwabzawa tsakanin janar-janar din soji biyu a Sudan ya bazu zuwa birane biyu na kasar da yaki ya daidaita.
Wasu shaidu sun bayyana cewa lamarin ya kara sanya fargaba a zukatan dubban mutanen da suka tsere wa tashe-tashen hankula a yankin Darfur.
Mutane da dama sun mutu a yankin yammacin Sudan da kuma babban birnin kasar Khartoum tun bayan barkewar yakin a ranar 15 ga watan Afrilu tsakanin sojojin Sudan da dakarun sa-kai na Rapid Support Forces (RSF).
Wasu ganau sun ce an samu barkewar sabon fada da yammacin ranar Alhamis a El Fasher babban birnin jihar Darfur ta Arewa, lamarin da ya kawo cikas ga kwanciyar hankali da aka samu na kusan watanni biyu a birnin wanda ya zama mafaka ga dubban mutanen da rikicin yankin ya tagayyara.
"Nan shi ne wuri mafi girma da fararen-hula wadanda suka rasa matsugunansu a Darfur suke, kusan mutane 600,000 ke zaune a El Fasher," a cewar Nathaniel Raymond na cibiyar binciken ayyukan jinkai a Makarantar Kiwon Lafiyar Jama'a ta Yale.
Wani mazaunin garin ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa: "Da dare ya yi, mun ji ana fada da manyan makamai daga gabashin birnin."
Shaidu sun kuma bayar da rahoton cewa fada ta barke a Al-Fulah, babban birnin jihar Kordofan ta Yamma mai iyaka da Arewacin Darfur.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama da shaidu da dama da suka tsere daga Darfur sun ba da rahoton irin kisan gillar da aka yi wa fararen-hula da hare-hare da kashe-kashen kabilanci, wadanda akasarin sojojin sa-kai ne da takwarorinsu Larabawa ke aikatawa.
Mutane da dama suna bi ta kan iyakar yammacin kasar don tserewa zuwa makwabciyar kasar Chadi, yayin da wasu kuma suka nemi mafaka a wasu yankunan Darfur, inda kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ke binciken zargin aikata laifukan yaki.
Yankin ya kasance wurin da aka dade ana gwabza kazamin fada tun bayan yakin da ya barke a shekarar 2003 da ya gamu da ayyukan hare-haren mayakan Janjaweed -- wadanda kungiyar RSF ta gada.
A yankin gabas, wani mazaunin Al-Fulah ya ce "RSF ta yi arangama da sojoji da kuma 'yan sanda, sannan an kona wasu gine-ginen jama'a a yayin musayar wuta".
"An wawashe kayayyakin cikin shaguna sannan kowanne bangare ya samu asarar rai, sai dai babu wanda zai iya zuwa inda gawarwakin suke," in ji wani shaida a Al-Fulah.
Rikicin ya raba 'yan Sudan kimanin miliyan hudu da muhallansu, kamar yadda alkaluman Majalisar Dinkin Duniya MDD suka nuna.
Kazalika ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 3,900 a fadin kasar, a cewar wani kiyasi na wata kungiyar tattara bayanai ta Armed Conflict Location & Event Data Project.