Shugaban kasar Turkoiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa tsarin da ya damka makomar dukkan duniya a hannun kasashe biyar ba zai dore ba, inda ya yi kira da a samar sauyi a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya “Da zai tafi da kowa”.
Shugaban ya ce “tsarin yanzu da ya mika makomar dukkan dan adam ga hannun kasashe biyar ba zai dore ba.
"Akwai bukatar gaggawa don yin kwaskwarima a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya yadda za a tafi da kowa tare.”
Ya kara da cewa, a yanzu Turkiyya na girbar alherin da ta shuka na manufar kasashen waje da ta mayar da hankali kan ayyukan jin kai da samar da sana’o’i, wanda a yanzu kasashen duniya da dama suna gaggawa don taimaka wa kasar bayan girgizar kasar da ta afku a ranar 6 ga Fabrairu.
Da yake tabo batun yakin Yukren da Rasha, Shugaba Erdogan ya bayyana yiwuwar samun yarjejeniyar zaman lafiya da za ta bai wa kowanne bangare damar janyewa, kuma hakan zai fitar da yankin daga kangin da aka jefa shi a ciki.