Erdogan ya bayyana alfaharinsa game da matakin Turkiyya na bayar da "agajin jinƙai" ga al'ummar Gaza./ Hoto: AA

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jinjina wa ƙungiyar Hamas game da matakan da take ɗauka na ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya mai ɗorewa, kana ya caccaki gwamnatin Isra'ila ta Firaiminista Benjamin Netanyahu kan hare-haren da take kai wa fararen-hula a Rafah da ke kudancin Gaza.

"Hamas ta ɗauki matakai na gaskiya kuma masu muhimmanci wajen tabbatar da daina buɗe wuta. Sai dai saɓanin hakan, martanin da gwamnatin Netanyahu ta mayar shi ne, kai hare-hare kan mutanen da masu da laifi a Rafah," in ji Erdogan lokacin da yake jawabi a taron duniya na Malaman Musulunci mai taken World Muslim Scholars Consultation Summit ranar Lahadi a Istanbul.

Ya ƙara da cewa, "Mun ga yadda waɗanda suke kiran kansu a matsayin ƙasar samar da 'yanci suka sauya zuwa masu kama-karya don rufe laifukan Isra'ila".

Kazalika Erdogan ya soki Isra'ila kan yadda take ƙara "faɗaɗa mamaya da cin zali," abin da ya yi sanadin "mutuwar rayukan da ba su da laifi", inda ya bayar da misali game da kisan da Isra'ila ta yi wa ƙananan yara 15,000 tare da sanya dubbai cikin uƙuba, da jikkata aƙalla mutum 80,000 da kuma raba fiye da mutum mmiliyan 2 da muhallansu.

"An take duk wasu dokoki da tsare-tsare da 'yanci na (Falasɗinawa) a yayin da duniya ta zuba idanu," in ji Erdogan, yana mai bayyana yankin Gaza a matsayin "matattarar mutanen da ake kashewa", inda ya kwatanta abin da ke faruwa a yankin da lamarin da ya faruwa a "Jamus a zamanin Hitler."

Haka kuma ya bayyana alfaharinsa game da matakin Turkiyya na bayar da "agajin jinƙai" ga al'ummar Gaza, wanda ya haɗa da kai "aƙalla tan 54,000" na kayan agaji.

Ya ce: "Mu ne ƙasar da muka fi bayar da agajin jinƙai zuwa Gaza."

TRT World