Yawan wadanda Isra'ila ta kashe a yaƙin Gaza ya kai 46,700 / Hoto: Reuters

Laraba, 15 ga watan Janairu, 2025

1115 GMT — Akalla karin Falasdinawa 62 ne aka kashe a hare-haren Isra’ila a Gaza a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu daga watan Oktoban shekarar 2023 zuwa 46,707, in ji ma’aikatar lafiya a yankin da aka yi wa kawanya.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta kara da cewa wasu 110,265 sun samu raunuka a harin da ake ci gaba da kai wa.

Ma'aikatar ta ce: "Sojojin Isra'ila sun kashe mutane 62 tare da raunata wasu 253 a kisan kiyashi shida na iyalai a cikin sa'o'i 24 da suka gabata.

0750 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 40 Gaza a yayin da ake dab da ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta

Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla 40 a ƙasa da awa 24 a hare-haren da ta kai sassa daban-daban na Gaza a yayin da take ci gaba da kisan ƙare-dangi duk da yunƙurin tsagaita wuta da ake yi.

Kamfanin dillanacin labarai na Falasɗinu, WAFA, ya ambato wasu majiyoyi suna cewa Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 13 tare da jikkata gommai a wani hari ta sama da ta kai gidansu a kudancin birnin Deir al-Balah da ke tsakiyar Gaza.

Kazalika wani hari da Isra'ila ta kai ta sama ya kashe Falasɗinawa bakwai a sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat, kana wani harin ta sama ya kashe wani Bafalasɗine a wani yanki na sansanin da ke tsakiyar Gaza.

Bugu da ƙari, Isra'ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa a hare-hare ta sama guda biyu da ta kai gidajensu a sansanin 'yan gudun hijira na Bureij.

Ƙarin labarai 👇

0944 GMT — Sojojin Isra'ila uku sun jikkata bayan tashin bam Gabar Yammacin Kogin Jordan

Wasu sojojin Isra'ila uku sun jikkata bayan da wani bam da aka dasa a gefen hanya ya tashi a Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamate, a cewar rundunar sojin ƙasar.

Wata sanarwar sojin ta ce biyu daga cikin sosjojin suna cikin mummunan yanayi bayan tashin bam din a cikin motar sojoji a lokacin da suke wani samame a Qabatiya kusa Jenin a Gabar Yammacin Kogin Jordan.

Daya sojan kuma bai ji rauni sosai ba.

0737 GMT — Rundunar sojin Amurka ta fitar da bidiyon harin da ta kai wa mayaƙan Houthi

Cibiyar Bayar da Umarni ta rundunar sojin Amurka (CENTCOM) ta fitar da bidiyo na harin da ta kai a ƙarshen shekarar da ta wuce a wuraren da ta bayyana a matsayin maɓiyar mayaƙan Houthi a Yemen.

"Ranar 30 da 31 ga watan Disamba, Cibiyar Bayar da Umarni ta rundunar sojin Amurka ta kai hare-hare a maɓoyar mayaƙan Houthi da Iran take goyon baya," kamar yadda CENTCOM ta bayyana a saƙon da ta wallafa a shafin X, tare da bidiyon.

Ta ƙara da cewa ta kai hari a "cobiyoyin bayar da umarni da tabbatar da tsaro da kuma wuraren samar da makamai da ma'ajiyunsu" na ƙungiyar.

TRT World