Ministan Harkokin Wajen Brazil Mauro Vieira ya buƙaci a samar da tsare-tsare a Majalisar Ɗinkin Duniya da wasu manyan cibiyoyin ƙasa da ƙasa yayin da ya soki yadda aka gaza kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe a daidai lokacin da ƙasarsa ta fara shugabanci a Ƙungiyar Ƙasashe Masu Ƙarfin Tattalin Arziki G20.
Mauro Vieira ya shaida wa takwarorinsa ministocin harkokin ƙasashen waje yayin buɗe taron Ƙungiyar G20 a birnin Rio de Janeiro a ranar Laraba cewa Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya gaza kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe kamar waɗanda ake yi a Ukraine da yankin Gaza da aka mamaye.
“Manyan cibiyoyin duniya ba su shirya yaƙi da matsalolin da ake fama da su ba, kamar yadda ake gani a raunin Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya dangane da yaƙe-yaƙe da ke faruwa,” in ji Vieira.
Ɗaya daga cikin manyan buƙatun Brazil da Shugaba Luiz inacio Lula da Silva yake so su ne samar da tsarin shugabanci na duniya kamar Majalisar Ɗinkin Duniya da Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya da manyan bankuna na ƙasa da ƙasa, inda yake so a riƙa samun wakilci mai ƙarfi daga ƙasashe masu tasowa.
Shugaba Lula da Silva ya nanata aniyarsa a ranar 18 ga watan Fabrairu ta faɗaɗa Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, inda ake duba yiwuwar ƙarin ƙasashen Afirka da na Latin Amurka da India da Jamus da kuma Japan.
“Ya kamata ku ƙara yawan mutane kuma ku kawo ƙarshen hawa kujerar na-ƙi a Majalisar Ɗinkin Duniya, saboda bai kamata a ce ƙasa ɗaya tilo ta hau kujerar na-ƙi kan wani batu da duka mambobin ƙasashe sun amince da shi ba,” in ji Lula yayin da yake ziyarar aiki a ƙasar Ethiopia.
Sai dai babu tabbas kan ko wannan yunkuri na Lula zai yi nasara, saboda a baya kasashen da suke da kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro sun kalubalantar hakan, wanda mataki ne da zai jawo rage musu karfin ikonsu.
“A halin yanzu, babu karsashin kawo sabbin tsare-tsare a Majalisar Dinkin Duniya, Majalisar Dinkin Duniya tana cikin matsala kuma tana iya yiwuwa wannan ba lokaci ne da ya dace a kawo sauye-sauye a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ba,” in ji wani masanin siyasa a Jami’ar Minas Gerais Lucas Pereira Rezende.
Vieira ya ce Brazil ta “damu matuka” dangane da yadda yake-yake ke kara bazuwa a fadin duniya – ba a Ukraine da Gaza ba kawai, hatta a wasu yankuna 170 na duniya, kamar yadda wani bincike ya bayyana.
Ministan Harkokin Wajen Brazil ya zargi Isra’ila da takwarorinta da “yin karya” kan batun rikicin Gaza.
Shugaba Lula ya gana da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken a babban birnin kasar Brasilia har tsawon sa’a biyu don su tattauna harkokin shugabancin a duniya da kuma sauran batutuwa.
Blinken wanda yake ziyarar kwana uku a Brazil da Argentina, daga bisani ya koma birnin Rio don halartar taron Kungiyar G20.
Shugabannin biyu sun kuma tattauna kan batun yakin da Isra’ila ke yi a Gaza da ta mamaye, ciki har da yin aiki cikin gaggawa don ganin an saki mutanen da ke tsare da kuma samar da taimakon jin-kai da kuma ba Falasdinawa fararen hula kariya, kamar yadda wata sanarwa daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta bayyana.
Sai dai ba su ce komai ba dangane da takaddamar diflomasiyyar da ta kunno kai tsakanin manyan aminanta biyu ba wato Isra’ila da Brazil bayan kalaman Lula na kwatanta kashe-kashen da Isra’ila ke yi wa a yankin da ta yi wa kawanya da kisan kiyashin Holocaust.
Yayin da yake magana da manema labarai a ranar Lahadi yayin taron Kungiyar Tarayyar Afrika a Ethiopia, Lula ya ce “abin da ke faruwa a zirin Gaza da kuma al’ummar Falasdinawa ba a taba ganin irinsa ba a tarihi. Kazalika, ya yi kama da yadda Hitler ya yi na kisan Yahudawa.”
A martanin Isra’ila kan Lula, kasar ta bayyana shugaban da “wanda ba a maraba da shi.” Kuma Isra’ila ta kira jakadan Brazil a kasar, inda ta bukaci ya nemi gafarar kasar.
A nasa martanin Shugaba Lula ya kira jakadan Brazil a Isra’ila don su tattauna kan batun.
An kafa Kungiyar G20 ne a shekarar 1999 don kawo manyan kasashe masu karfin tattalin arziki waje daya.
Da farko an kafa ta ne don batutuwan tattalin arziki, amma daga bisani ta shiga cikin harkokin siyasar duniya.