1628 GMT — Babu wata alaka da Isra'ila har sai an tsagaita wuta a Gaza - Jakadiyar Saudiyya a Amurka
Saudiyya ba za ta iya ci gaba da tattaunawa kan wata muhimmiyar yarjejeniya ta amincewa da Isra'ila ba har sai an tsagaita wuta a Gaza, in ji jakadiyar masarautar a Amurka.
Gimbiya Reema bint Bandar al Saud ta shaida wa wani taron tattalin arziki na duniya a Davos, Switzerland cewa, "Ina ganin abu mafi muhimmanci da ya kamata a gane shi ne, masarautar ba ta sanya al'ada a cikin muradun manufofinta ba, ta sanya zaman lafiya da wadata a cikin muradun manufofinta."
"Masarautar ta fito fili. Duk da yake akwai tashin hankali a kasa kuma ana ci gaba da kashe-kashen, ba za mu iya magana game da abin da zai faru gobe ba."
Saudiyya, wacce kasa ce mai dauke da mafi tsarkin wurare na Musulunci, ba ta taba amincewa da Isra'ila ba, kuma ba ta shiga yarjejeniyar Abraham da Amurka ta kulla a shekarar 2020 ba, wadda ta sanya makwabtanta na yankin Gulf kamar su Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa gami da Maroko suka kulla alaka ta yau da kullun da Isra'ila.
1337 GMT — Yawan mutanen da aka kashe a hare-haren Isra'ila a Gaza ya kai 24,600
Jami'an kiwon lafiya na Falasdinawa a Gaza sun ce akalla mutane 24,620 ne suka mutu zuwa yanzu a hare-haren da Isra'ila ta kai kan Zirin tun daga ranar 7 ga Oktoba.
Sanarwar da ma'aikatar lafiya ta fitar ta ce an kuma jikkata mutane 61,830 a yankin Falasdinu a yayin wannan ta'asar.
0806 GMT — An sake kashe gomman mutane a harin sama da Isra'ila ta kai Gaza
Hare-haren sama da Isra'ila ta kai cikin dare sun sake kashe gomman mutane, ciki har da waɗanda ta kai a kudancin yankin Gaza, inda Isra'ilan ke zafafa hare-harenta na soji, kamar yadda Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta faɗa.
Sabbin hare-haren dai na zuwa ne a daidai lokacin da magungunan mutanen da mayakan suka yi garkuwa da su da kuma sabbin kayan agaji ga fararen hula suka shiga yankin Falasdinu karkashin wata sabuwar yarjejeniya.
Ma'aikatar ta ce an kashe mutum 93 da suka haɗa da mutum 16 ƴan gida ɗaya da aka kashe a birnin Rafah da ke kudancin Gazan, wajen da mutane da yawa suka tsere daga cikinsa.
"Harin ya kashe mutum 16, ciki har da mata da yara, sannan mutum 20 sun jikkata," in ji ma'aikatar.
0706 GMT — UAE ta yi alkawarin ba da gudunmawar dala miliyan 10 ga fannin lafiya na Gaza
"Cibiyar Mohammed bin Rashid Al Maktoum Global Initiatives (MBRGI) ta yi alkawarin ba da tallafin kusan dala miliyan 10 don taimakon fannin lafiya na Gaza," kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Emirates (WAM) ta rawaito.
Waɗannan tallafi "za a ba da su ne da burin samar da ingantattun kayan aiki na fannin lafiya a Gaza, musamman ga yara da yaƙin yake mummunan tasiri a kansu," ta ce.
"Alkawarin ya zo ne a wata wasiƙar yarjejeniya da aka cimma tsakanin MBRGI da Hukumar Lafiya ta Duniya, da nufin tallafawa ayyukan jinƙai tare da samar tsarin ba da agajin gaggawa a Zirin Gaza," kamfanin dillancin labaran ya ƙara da cewa.
0151 GMT — Amurka ta harba makamai masu linzami a Yemen
Amurka ta sake harba wasu makamai masu linzamin a sansanonin ƙungiyar Houthi, kamar yadda jami'an Amurka suka ce, lamarin da ya zamo karo na huɗu kenan a cikin kwanaki kaɗan da ta kai hari kai tsaye a kan ƙungiyar ta Yemen, a lokacin da yaƙin Isra'ila a Gaza ke ci gaba da watsuwa a Gabas ta Tsakiya.
Hare-haren dai na zuwa ne bayan da aka harba wani jirgi mara matuki daga yankin da 'yan Houthi ke iko da shi a kasar Yaman, ya kuma kai hari kan tsibirin Marshall, mallakin Amurka da kuma M/V Genco Picardy a mashigin Tekun Aden.
A ranar Laraba, kakakin Houthi Mohammed Abdelsalam ya shaida wa tashar talabijin ta Al Jazeera cewa, kungiyar za ta ci gaba da kai hare-hare kan jigilar kayayyaki a Tekun Maliya, bayan matakin da Amurka ta dauka na mayar da kungiyar cikin jerin sunayen 'yan ta'adda.
"Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen kai hare-hare kan jiragen ruwa ko na Isra'ila da ke kan hanyar zuwa tashar jiragen ruwa na Falasdinu da ta mamaye...domin goyon bayan al'ummar Falasdinu," kamar yadda ya shaida wa kafar yada labaran kasar Qatar.
0054 GMT — Houthis sun sha alwashin ci gaba da kai hari kan jiragen ruwa masu alaka da Isra'ila
Dakarun Amurka da na Birtaniya sun kaddamar da farmaki karo na hudu a yankuna hudu na kasar Yemen, in ji kungiyar Houthi, tana mai cewa za ta ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwa masu alaƙa da Isra'ila.
Tashar talabijin ta Al-Masirah ta Houthis ta ce, "Amurka da Birtaniya sun kai hari kan sansanonin Al-Hudaidah da Taiz da Dhamar da Al-Bayda da Saada," in ji tashar talabijin ta Houthis ta Hudaida, birnin Taez da sauran wurare.
"Za mu ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwan Isra'ila da ke kan hanyar zuwa tashar jiragen ruwa na Falasdinu da ta mamaye, ko ta yaya, duk da hare-haren Amurka da Birtaniya ke kokarin hana mu yin hakan."