1407 GMT — Asibitin Al-Aqsa ya karɓi gawawwakin mutum 94 da Isra'ila ta kashe da safiyar Asabar
Adadin Falasɗinawan da Isra’ila ta kashe a sansanin gudun hijira na Nuseirat ya ƙaru zuwa 210, inda sama da 400 suka jikkata, kamar yadda ofishin watsa labarai na Gaza ya tabbatar.
"An kawo wasu shahidai 210 da mutum fiye da 400 da suka jikkata zuwa Asibitin Al-Aqsa sakamakon mummunan kisan kiyashin da Isra'ila ta yi a sansanin Nuseirat," in ji ofishin yada labaran.
Ofishin ya kara da yin kira ga kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa da su ceci asibitin shahidan Al-Aqsa tare da samar masa da kayayyakin masarufi da janareto don tabbatar da ci gaba da gudanar da aikinsa.
1217 GMT — Adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a Gaza ya haura 36,800
Akalla Falasdinawa 36,801 ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa a Gaza tun a watan Oktoban da ya gabata, in ji ma’aikatar lafiya a yankin da aka yi wa kawanya.
Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta kara da cewa an kuma jikkata wasu mutane 83,680 a harin.
Sanarwar ta ce "Hare-haren Isra'ila sun kashe mutane 70 tare da jikkata wasu 150 a cikin sa'o'i 24 da suka wuce."
“Har yanzu mutane da dama na makale a karkashin baraguzan gine-gine da kuma kan tituna yayin da masu ceto suka kasa kai musu dauki,” kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.
1033 GMT — Isra'ila ta kashe mutum 11 da jikkata da dama a wani sabon hari da ta kai Gaza
Akalla Falasdinawa 11 ne aka kashe tare da jikkata wasu da dama a hare-haren da Isra'ila ta kai a tsakiyar Gaza.
Kamfanin dillancin labaran na WAFA ya ruwaito akwai wasu gommai da suka jikkata sakamakon wannan harin na safiya.
Rahotannin sun bayyana cewa jami’an kare farar hula sun yi ƙoƙarin gano gawawwaki biyar daga ciki har da na yara da mata daga cikin ɓaraguzai, bayan da sojojin Isra’ila suka kai hari a gidan iyalan Mhanna da ke unguwar Sheikh Radwan.
Sannan kuma hare-haren na Isra’ila sun kai hari wani gida da ke sansanin gudun hijira na Al Bureij wanda ke a tsakiyar Gaza inda mutum shida suka rasu da jikkata da dama.
1010 GMT — Masu zanga-zanga na shirin yi wa Fadar White House 'ƙawanya' kan rikicin Gaza
Magoya bayan Falasɗinu da ke fafutikar ganin an kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza da kuma goyon bayan da Amurka ke bayarwa, na shirin yin ƙawanya ga Fadar White House ta Amurka a ƙarshen makon nan.
Ƙungiyoyin gwagwarmaya irin su CODEPINK da Council on American Islamic Relations a ranar Juma’a sun bayyana cewa an shirya yin zanga-zanga a ranar Asabar, a lokacin da za a cika wata takwas ana yaƙin Gaza wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane da kuma jefa mutane cikin bala’i da yunwa.
Amurka wadda babbar ƙawar Isra’ila ce, an ta yi mata bore iri-iri a Washington da kuma wurare da ke kusa da White House, zuwa rufe hanyoyi kusa da tashoshin jirgin ƙasa da kwalejoji.
Akalla jami'ai takwas ne suka yi murabus daga gwamnatin shugaba Joe Biden, saboda rashin amincewarsu da manufofinsa. Masu zanga-zangar sun kuma dakile wasu lamuran yakin neman zaben Biden.