Isra'ila na ci gaba da Falasɗinawa a kullum waɗanda akasarinsu yara ne da mata. / Hoto: Reuters

1605 GMT — Asibitin Shahidai na Al-Aqsa da ke Deir al-Balah a tsakiyar Zirin Gaza ya yi gargadi game da matsanancin karancin man fetur da magunguna, yana mai jaddada cewa hakan na yin barazana ga mutane da dama da suka jikkata a yakin da Isra'ila ke ci gaba da yi tun watan Oktoban bara.

Mai magana da yawun asibitin Khalil Al-Dakran ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu hadarin da ke tattare da dakatar da dakunan tiyata saboda tsananin karancin magunguna da kuma man fetur.

Al-Dakran ya yi gargadin cewa idan dakunan tiyata sun daina aiki, marasa lafiya da dama za su iya mutuwa

0835 GMT — Isra’ila ta kashe wani ɗan jarida a harin da ta kai Gaza a ranar Asabar, wanda hakan ya kawo adadin ‘yan jaridar da ƙasar ta kashe zuwa 161 tun daga 7 ga watan Oktoba.

Majiyoyi na kiwon lafiya sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa sojojin Isra’ila sun kai hari gidan Muhammad Jasser da ke arewacin Zirin Gaza.

Harin ya yi sanadin mutuwar Jasser da matarsa da ‘ya’yansa biyu, wanda hakan ya kawo adadin ‘yan jarida Falasɗinawa da Isra’ila ta kashe a Gaza zuwa 161.

Fiye da Falasdinawa 38,800 aka kashe tun daga lokacin, akasari mata da yara, sannan sama da 89,400 suka jikkata, a cewar hukumomin lafiya na yankin.

2051 GMT — Babban Mai Bayar da Shawara kan Tsaron Ƙasa a Fadar White House Jake Sullivan ya ce shugaban Amurka Joe Biden da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu za su yi taro don tattaunawa kan hanyoyin da za a bi don cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da aka mamaye tare da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su.

"Babban abin da taron da za yi tsakanin Shugaba Biden da Firaminista Netanyahu zai mayar da hankali a kai shi ne tsagaita wuta da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su," in ji Sullivan a jawabin da ya yi a wurin taro kan tsaro na Aspen Security Forum a Colorado.

Ya ce Biden zai matsa wa Netanyahu wajen ganin "an amince da wannan yarjejeniya nan da makonni masu zuwa."

2248 GMT — Sojojin Isra'ila sun kashe wani matashi Bafalasɗine a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan

Sojojin Isra'ila sun kashe wani matashi Bafalasɗine a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan. Gidan talbijin mai suna Palestine TV ya ce sojojin Isra'ila sun harbe Ibrahim Zaqeeq, ɗan shekari 19, a ka a unguwar Beit Ummar.

Ya ƙara da cewa an sako Zaqeeq daga kurkuku ne makonni biyu da suka wuce kuma shi kaɗai iyayensa suka haifa.

Ganau sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu Agency cewa wasu sojojin Isra'ila sun kai samame unguwar Beit Ummar sannan suka buɗe wuta kan Falasɗinawa, inda suka jikkata Zaqeeq da wasu Falasɗinawa bayan sun fesa musu hayaƙi mai sa ƙwalla. Daga bisani ne ya mutu.

2125 GMT — An yi zanga-zanga a Tunisia da Morocco kan yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza

Dubban mutane sun sake gudanar da jerin zanga-zanga a Tunisia da Morocco, don yin tir da Isra'ila kan yaƙin da take ci gaba da yi a Gaza.

A Tunis, babban birnin Tunisia, dubban masu zanga-zanga sun taru a babban titin Habib Bourguiba domin nuna goyon baya ga Falasɗinawa.

Masu zanga-zangar suna riƙe da tutocin Falasɗinu da na Tunisia inda suka riƙa rera taken "A Bai wa Falasɗinawa 'Yanci" da kuma "Munafukan ƙasashen duniya sun cinna wuta a Gaza da Falasɗinu."

An gudanar da irin wannan zanga-zanga a wasu biranen Morocco, ciki har da Rabat, Fez, Meknes, Tangier, Kenitra, Nador, Ahfir, Taroudant da Agadir.

TRT Afrika da abokan hulda