Shugabannin Turai da suka gana a Budapest sun bukaci Donald Trump da ya nisanci yakin tattalin arziki, ya kuma ci gaba da goyon bayan Ukraine tare da kawar da kai daga rusa tsarin da duniya ke tafiya a kai yau bayan nasarar lashe zaben shugaban kasar Amurka.
"Na yarda da jama'ar Amurka," in ji Shugaban Majalisar Turai Charles Michel a ranar Alhamis a yayin da shi da sauran su suka bukaci Trump da ya ci gaba da goyon bayan Ukraine, a lokacin da shugabannin Turai kusan 50 suka taru don gana wa a Budapest.
"Sun san suna son a nuna tsaurarawa a lokacin da muke mu'amala da gwamnaocin da ke kama-karya. Idan Amurkawa suka yi sako-sako da Rasha, to me zai faru da China kuma?"
Nasarar Trump babban kalubale ne ga Trai, an bude wani sabon shafi na rashin tabbas a lokacin da nahiyar ke fama da matsalar hadin kai, kuma aka raunana manyan mabobinta biyu Jamus da Faransa.
A tsawon wa'adinsa na farko, alakar Trump da shugabannnin Turai ba ta yi kyau ba, kuma dawowar sa kan mulki ya zo da tantama kan goyon bayan Amurka ga Ukraine don kalubalantar Rasha, rawar da Amurka ke taka wa a kawancen NATO da kuma makomar kudaden harajin shigar da kaya Amurka daga kasashen waje.
A gefe guda, shugabar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce a yanzu ya rage na Tarayyar Turai d ata hada kai. Babu wata kasa mambar Tarayyar Turai da ita kadai za ta iya magance kalubalen da ke tafe, in ji ta.
Game da Ukraine kuma ta ce "Duk yana daga manufofinmu cewa masu kama-karya a duniyar nan su samu sako karara cewa ba su da 'yancin amfani da karfi, sai dai aiki da doka da oda."
Yaƙin kasuwanci
Da yawan shugabannin sun ce suna sauraron ganin sun yi aiki tare da Trump.
Firaministan Hungary da ke karbar bakuncin taron, Viktor Orban, na daya daga shugabannin Tarayyar Turai da ke da kyakkyawar fahimtar juna da Trump, kuma ya ce zai zuba ruwa a kasa ya sha idan Trump ya yi nasara.
Jami'an diflomasiyya sun yi ta yada jita-jitar cewa Orban na iya shirya yadda Trump zai yi jawabi ga shugabannin Turai ta hanyar sadarwar bidiyo.
Amma wasu kuma ba su damu da matsalolin ba, ciki har da batun yadda Trump yake murkushe abokansu a fannin kasuwanci.
"An san Shugaba Trump da zama ƙuli-ƙuli ba a san gabanka ba ta yadda ba a iya hasashen me zai aikata, a saboda haka muna bukatar tattaunawa," in ji Firaministan Luxembourg, Luc Frieden. "Za mu nemi mu tattauna, amma ba za mu hakura da akidunmu ba."
Firaministan Finland, Petteri Orpo ya ce ya damu da batun yiwuwar yakin kasuwanci; "Bai kamata a bar hakan ta faru ba," in ji shi.
"A yanzu bari m yi yunkurin samun iko kan Amurka da manufofin Trump masu zuwa ta yadda za su fahimci hatsarin da ke tattare da hakan."
Da take kara bayyana damuwa game da batutuwan taron na Budapest, gwamnatin Jamus da jam'iyyu uku suka kafa sun samu matsala a kawancen nasu a ranar Laraba bayan da Firaminista Olaf Scholz ya kori ministan kudi wanda hakan ya bayar da kofar gudanar da sabon zabe.
"Wani da yake tabbas, shi ne Turai ba ta da karfi idan babu Jamus," in ji shugaban Majalisar Dokokin Tarayyar Turai Roberta Metsola.
Taron zai fara da ganawar shugabanni da kuma 'yan siyasar Turai da ma na kasashen da ba mambobi ba, irin su Birtaniya, kuma ana sa ran za su sabunta kudirinsu na goyon bayan Ukraine, sannan za a yi wasu zaman kan gudun hijira da amincin tattalin arziki.
Mark Rutte, shugaban NATO, ya ce yana da muhimmanci a kalli Ukraine a matsayin matsalar da ta tsallake iyakokin Turai, inda ya bayyana hadin kan Rasha da Koriya ta Arewa a matsayin barazana ba wai bangaren NATO na Turai ba, har ma ga Amurka".