1526 GMT –– Yaran Gaza suna rayuwa 'cikin tsoro da firgici mara iyaka' saboda hare-haren Isra'ila: Hukumar MDD
Yaran Gaza suna rayuwa 'cikin tsoro da firgici mara iyaka' sakamakon mummunan farmakin da Isra'ila ke kaiwa a yankin Gaza da ke gabar teku, in ji hukumar kula da 'yan gudun hijirar Falasdinu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA).
Sanarwar ta kara da cewa, "Harin bama-bamai da gudun hijira ala tilas da rashin abinci da ruwa da kuma rashin samun ilimi suna cutar da al'umma baki daya."
Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kungiyoyin taimakon jinƙai na ci gaba da aiki "don ba da taimako da kyakkyawan fata ga yara a Gaza."
1525 GMT –– Ana zargin an dasa bam a wani kamfanin Isra’ila da ke Sweden –– ‘Yan sanda
‘Yan sandan ƙasar Sweden sun ce suna zargin an dasa bam a wajen wani kamfanin fasahar soji na Isra’ila a Gothenburg, kuma akwai alamar an dasa shi ne don tayar da kamfanin.
An gano wani "abu da ake zargin na fashewa ne" a wajen ofisoshin Elbit Systems, wanda ke ƙera na'urorin jirage marasa matuka, a birni na biyu mafi girma a Sweden da sanyin safiyar Litinin, in ji 'yan sanda.
‘Yan sanda sun killace wurin na ‘yan sa’o’i kadan yayin da aka kira tawagar da ta ƙware wajen cire bama-bamai ta ƙasar zuwa wurin da lamarin ya faru, kuma an cire abin lafiya.
1510 GMT — MDD ta koka kan irin kisan da ake yi a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan
Shugaban Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya buƙaci a kawo ƙarshen rikicin da ake yi a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, inda ya ce “hankali ba ya ɗaukar abin da ke faruwa.
Sama da Falasɗinawa 500 aka kashe a yammacin kogin tun daga 7 ga watan Oktoba.
A wata sanarwa da ya fitar, Volker Turk ya caccaki Israila inda ya ce aƙalla Falasɗinawa sama da 500 aka kashe a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, waɗanda sojoji da ‘yan kama wuri zauna na Isra’ilar suka halaka.
1820 GMT — Scholz na Jamus ya bukaci Netanyahu da ya inganta yanayin Gaza
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bukaci firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ya ci gaba da inganta ayyukan agaji da kiwon lafiya a Gaza.
A wata tattaunawa ta waya da ya yi da Netanyahu, Scholz ya kuma sake bayyana gamsuwarsa ga shirin yarjejeniyar tsagaita wuta mai mataki uku da Joe Biden ya gabatar, kamar yadda mai magana da yawun Steffen Hebestreit.
Kazalika shugabannin biyu sun yi musayar ra'ayoyi a kan yanayin da ake ciki a yankin, inda Scholz ya bayyana damuwarsa a kan ka da hakan ya watsu ya zama rikicin yanki.