An sake kama dalibi dan kasar Chadi wanda ya fitar da wani sautin murya a watan da ya gabata na wasu kalaman nuna wariya da ‘yan sandan Faransa suka yi.
Wani rahoto da tashar BFMTV ta fitar ya ce a yayin zanga-zangar adawa da matakan gwamnatin Faransa kan tsarin fansho da aka yi a birnin Paris ne ‘yan sandan Faransa suka kama matashin mai shekara 23.
Rahoton ya kara da cewa an kama Adoum ne kawai saboda yana kusa da wasu mutum biyu da suka yi yunkurin kona kwandon sharar da ke kan hanya.
An daure Adoum da sauran mutanen biyu.
A ranar 20 ga Maris an kama Adoum a yayin zanga-zangar kin jinin sauya tsarin fansho, kuma bai ji da dadi ba a hannun ‘yan sandan Faransa.
A wani faifan murya da kafafen yada labaran Faransa suka fitar an jiyo ‘yan sanda na nuna wariya ga Adoum wanda ya zarge su da marin sa.
Cibiyar ‘yan sanda mai cike da rikici
‘Yan sandan sun yi kalamai munana na batsa da nuna wariya, inda daya daga cikin su ya fada wa mai zanga-zanga su kula da zuba idanu a lokaci na gaba saboda za su iya samun kawunansu a notar daukar marasa lafiya zuwa asibiti.
An ji dan sandan na cewa “Zan ji dadin ganin na karya kafafuwanka”.
Daga baya an saki Adoum ba tare da wata tuhuma ba.
Bayan korafin da Adoum ya shigar ne hedikwatar ‘yan sandan Faransa ta fara gudanar da bincike kan lamarin.
‘Yan sandan Kwantar da Tarzoma da ke Hawa Babura (BRAV-M), na yawan janyo ka-ce-na-ce sakamakon zargin su da ake yi da nuna wariyar launin fata da amfani da karfin da ya wuce ka’ida da kuma gallazawa.
'Yan siyasar Faransa sun sanya hannu kan wani korafi a watan Mayu kan a rufe wannan sashe na ‘yan sadan kasar.
Amma shugaban ‘yan sandan Paris Laurent Nunez ya ce batun rufe sashen ma bai taso ba.