Hanaan Shaidan da danta Wadea Al Fayoume suna zaune a kasan benen gidan kusan tsawon shekara biyu kafin aukuwar lamarin./ Hoto: OTHER

Wani mutum a birnin Chicago na jihar Illinois a Amurka ya daba wa wani yaro dan shekara 6 wuka inda ya mutu sannan ya jikkata mahaifiyarsa a wani harin nuna kiyayya ga addinin Musulunci da iyalansa suke yi kan batun rikicin Isra'ila da Falasdinu.

An caka wa yaron wuka har sau 26 tare da yankarsa da wani zarto mai tsawon inci bakwai, a cewar sanarwar da Ofishin 'yan sanda na Gundumar Will ya fitar.

Kazalika mahaifiyar yaron mai shekaru 32 ta samu raunuka da dama, ko da yake an yi sa'a ta tsira da ranta a harin da aka kai musu ranar Asabar a garin Plainfield, mai nisan kilomita 64 daga yankin kudu maso yammacin Chicago.

"Masu bincike sun tabbatar da cewa an kai wa wadanda lamari ya shafa harin ne saboda kasancewarsu Musulmai da ke da alaka da rikicin Gabas ta Tsakiya tsakanin Hamas da Isra'ila," in ji 'yan sanda.

“Mun yi matukar kaduwa bisa wannan labari da muka samu kan yadda wani mai gida a birnin Chicago ya bayyana kiyayyarsa a kan Musulmai da Falasdinawa ta hanyar kutsa kai cikin gidan wasu iyalai da ke haya a gidansa tare da kai musu hari da wuka, inda ya raunata matar gidan da kuma kashe danta Wadea Al Fayoume mai shekaru 6,” a cewar wani sako da kungiyar majalisar inganta dangantaka tsakanin Musulmai da Amurka (CAIR) ta wallafa a shafinta na X.

"Dole ne a dakatar da 'yan siyasa da kafafen yada labarai da kuma shafukan sada zumunta da wadanda ke yada kalamai na nuna kyama da kiyayya ga Falasdinu," a cewar kungiyar.

"Bayan ya kwankwasa kofa ne ya yi yunkurin shake ta, sannan ya ce 'ku Musulmai, dole ne ku mutu,' kamar yadda shugaban ofishin CAIR na Chicago, Ahmed Rehab, ya shaida wa manema labarai, yana mai nuni kan sakon da matar da a kashe danta ta tura wa mijinta yayin da take kwance a gadon asibiti.

An tuhumi maharin, Joseph Czuba, mai shekaru 71 da laifin kisan kai da yunkurin kisan kai da kuma amfani da mugun makami don kai hari da wasu laifuka biyu kan nuna kyama, in ji ofishin 'yan sanda.

'Kaduwa da bakin ciki'

Shugaban Amurka Joe Biden ya yi tir da kisan da aka yi wa Bafalasdinen kuma Ba'amurke.

"Ni da (Uwargidana) Jill mun kadu da jin wannan labarin kisan gillar da aka yi wa yaron dan shekara shida da kuma yunkurin kashe mahaifiyarsa a gidansu a garin Illinois a jiya," in ji Biden a cikin wata sanarwa da ya fitar.

"Irin wannan mummunar aika-aikar nuna kiyayya ba ta da wurin zama a Amurka kuma ta ci karo da muhimman dabi'unmu na kasa: na samun 'yanci da damar gudanar da ibada," in ji shi.

Biden ya bukaci Amurkawa da su hada kai don yakar dabi'ar nuna kyamar Musulunci a sakonsa kan batun kisan gillar da ya faru.

"A matsayinmu na Amurkawa, dole mu hada kai wajen yakar kiyayya ga Musulunci da duk wasu nau'ukan son zuciya da nuna kyama. Na sha bayyana cewa ba zan yi shiru ba kan batun nuna kiyayya. Dole mu tsaya a kan wannan matsayar, babu wani wuri a Amurka da aka yarda a nuna kyama ga kowa," in ji shi.

TRT World