1048 GMT — An kammala sauke tan 200 na kayan agajin da za a raba wa jama'ar Gaza
Wata kungiyar agaji ta Amurka ta ce tawagarta a yankin Gaza da yaki ya ɗaidaita, ta kammala sauke kayan agajin na farko a teku domin isa yankin da aka yi wa kawanya.
"An sauke dukkan kaya kuma ana shirin rarrabawa a Gaza," in ji World Central Kitchen a cikin wata sanarwa, inda ta ƙara da cewa tallafin ya kasance "kusan tan 200 na abinci."
Jirgin ruwan ya taso ne daga tashar jiragen ruwa ta Larnaca ta gwamnatin Cyprus ta Girka kuma ta isa gabar Gaza a ranar Juma'a.
0230 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fararen-hula 80 a sabbin hare-hare da ta kai Gaza — Falasɗinu
Jiragen yaƙin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa aƙalla 80 sannan suka jikkata wasu a hare-haren tsakar dare da suka kai a gidaje da gine-ginen gwamnati a Gaza, a cewar kafofin watsa labaran Falasɗinu da hukumomi.
Kamfanin dillancin labarai na Falasɗinawa (WAFA) ya ce Isra'ila tana ci gaba da kai hare-hare babu ƙaƙƙautawa a yankuna daban-daban, ciki har da sansanin ƴan gudun hijira na Nusairat da Birnin Gaza.
Sojoji sun jefa bama-bamai a gidajen da ke Titin Al Jala, inda ɓaraguzan gine-gine suka danne jama'a. Sun rusa wani gini mai hawa bakwai kusa da Asibitin Al Shifa da ke Birnin Gaza, inda Falasɗinawan da suka rasa gidajensu suke samun mafaka, abin da ya kai ga mutuwar gomman mutane da jikkatar wasu.
Ma'aikatan agaji sun zaƙulo gawawwaki biyar na Falasɗinawa daga ɓaraguzan gine-gine, yayin da ake ci gaba da aikin ceto.
Kazalika Falasɗinawa akalla biyar sun mutu yayin da dama suka jikkata lokacin da Isra'ila ta kai hari a wani gida da ke Tuffah a Birnin Gaza.
A yankin Nasr, sojojin Isra'ila sun kashe mutane da dama lokacin da suka buɗe wuta a wani gida, a cewar ofishin watsa labarai na gwamnatin Gaza. Daga bisani sun kai hari a sansanin ƴan gudun hijira na Nusairat, inda suka kashe fararen-hula aƙalla 36.
0115 GMT — Jiragen yaƙin Isra'ila sun kashe mata masu ciki da ƙananan yara 36 a sabbin hare-haren da suka kai Gaza
Jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hare-hare a sansanin ƴan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza, inda suka kashe Falasɗinawa fararen-hula aƙalla 36, gaibinsu ƙananan yara da mata masu ciki, a cewar wata sanar da hukumomn Falasɗinu suka fitar.
"Sojojin mamaya na Isra'ila sun kai harin bama-bamai a gidan iyalan al Tabatibi da ke yammacin sansanin ƴan gudun hijira na al Jadid a Nuseirat (a tsakiyar Zirin Gaza), inda suka kashe Falasɗinawa 36, galibinsu ƙananan yara da mata masu ciki," in ji sanarwar.
Sojojin sun kai hari kan gidaje aƙalla 12 na fararen-hula a Gaza, a cewar sanarwar.
Ta ƙara da cewa, "Muna ɗora alhakin ƙaruwar kisan ƙare-dangi da ake yi wa fararen-hula kan gwamnatin Amurka, da manyan ƙasashen duniya da Isra'ila the international. Su ne kanwa uwar gami na waɗannan laifukan yaƙi da ake aikatawa."