A baya-bayan nan jihohi biyar ne a Indiya suka sha fama da rikicin addini /Hoto: (Altaf Qadri / AP Archive)

An kama fiye da mutum 50 a Jihar Jharkhand da ke yankin gabashin Indiya bayan barkewar wani rikicin addini tsakanin Musulmai da mabiya addinin Hindu.

Prabhat Kumar, wani babban jami'in 'yan sanda a yankin, ya tabbatar da batun kamen ga manema labarai a ranar Litinin.

“An aike tawagar 'yan sanda da jirage marasa matuka masu sa ido a yankunan da ake rikicin, kuma ana shawo kan lamarin," kamar yadda Kumar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na ANI.

Hukumomin gundumar sun katse intanet na wucin gadi tare da haramta taron jama'a da suka wuce biyar a yankin Jamshedpur, a kokarinsu na dakile ruruwar rikicin.

A ranar Lahadi ne rikicin addinin ya barke a yankin kan zargin lalata wata tuta wacce ake amfani da ita wajen bukukuwan addini na Hindu.

Karuwar rikicin addini

Wata kungiya ta mabiya Hindu ta yi zargin cewa ta gano tutar an dukunkune yankan nama a cikinta. Mabiya Hindu da dama ba sa so ana cin naman shanu.

Daga nan ne sai mabiya addinin Hindu suka bazama kan tituna suna zanga-zanga, inda suka bukaci sai an dauki mataki a kan wadanda suka aikata hakan.

A cewar 'yan sanda, masu zanga-zangar sun yi ta jifan shaguna da ababen hawa da ke wucewa ta yankin.

A baya-bayan nan jihohi biyar ne a Indiya suka sha fama da rikicin addini a yayin bukukuwan addini na Hindu a watan da ya gabata. A kalla mutum biyu aka kashe a wadannan lamaran.

Tun shekarar 2014 rikicin addini ke karuwa a Indiya - lokacin da Firaminista Narendra Modi ya zama shugaban kasar - inda ya bayyana akidar bai wa addinin Hindu fifiko.

TRT World